Ilimi Kogi Ne Filin Shirin asmsa tambayoyin masu sauraron daga Ustaz Yusuf Ali

Filin amsa tambayoyin masu saurare daga Ustaz Yusuf Ali
Juma'a 21 ga Jimada Sani 1423                



 Maigida da Uwargida | TAMABAYA TA 1  | TAMBAYA TA 2 | TAMBAYA TA 3 | TAMBAYA TA 4 | TAMBAYA TA 5 | TAMBAYA TA 6 | TAMBAYA TA 7 
Ilimi Kogi Ne | TAMBAYA TA 8
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
Ilimi Kogi Ne:

Shirin Ustaz Dakta Yusuf Ali

Addu'ar samun miji da sasanta ma'aurata

Mai karatu wannan shafin zai rika kawo maka shirin gidan rediyon jihar Kano mai suna Ilimi Kogi Ne da Ustaz Dakta Yusuf Ali ke yi a gidan rediyon duk mako, insha Allah. Wannan wanda aka buga a jaridar DILLALIYA ta 21 ne.

TAMBAYA: Wata daliba ce keso ta yi wa Malam tambaya. Muna tambayar Malam ne wata sallah da ya yi bayani cewa in an yi sallar an idar, za a yi wa Allah godiya, to yaya ake yi wa Allah godiyar? Kuma Malam ya ce a yi wa Allah yabo, to yaya ake yabon Ubangiji? Kuma Malam ya ce in mutum zai kwanta barci ya karanta "Tabara," mutum zai iya karantawa kafin ya kwanta, ko kuwa a'a sai ya kwanta a shimfidarsa zai yi wannan addu'ar? Kuma Malam ya yi bayanin wani yaro wanda idan ya kangare akan karanta masa salatun tunajjina da kuma "kulhuwallahu", to da kuma menene? Malam mun kasa gane abin da ka fada na karshe, shi ne muke so Malam ya dada yi mana bayani. Kuma muna wa Malam godiya, Allah ya saka masa da alheri a kan taimaka wa addinin Musulunci da yake yi.

DAKTA YUSUF ALI: Ina jin tana nufin sallah ta neman biyan bukata wacce Annabi (SAW) shi ne ya ba da wannan sallar; wanda yake cewa idan mutum yana da bukata a wajen Allah ko a wajen wani dan Adam, to ya yi alwala ya yi sallah raka'a biyu. In ya idar ya yabi Allah, ya gode masa, ya girmama shi, kuma ya yi salati ga ManzonSa (S), sannan kuma sai ya karanta addu'ar La ilaha illallahul Halimul Karim. Alhamdu lillahi Rabbil alamin. As'aluKa Mujibatul hamdi…" har zuwa karshen "ya Arrahamanir rahim." To sannan sai ya roki bukatar tasa.

Ustaz Yusuf Ali tare da Shaikh Abdulnasir na Jami'ar Azhar

Salatin Annabi dai za a yi da kowace irin siga; yaba ma Allah, mutum yana iya karanta Fatiha. Ni nakan dunkule irin wadannan abubuwa, wani lokacin nakan karanta misalin ayoyi shida na farkon Suratul Hadid, hudu na karshen Hashari. Za ki ga wadannan duk sun jumlace yabo da godiya da kuma girmama Allah (T). Za a ce "Huwal Awwalu wal Akhiru waz Zahiru wal Badinu…"; to irin wadannan za ki ji ke ma a jikinki kina yaba ma Allah sosai da sosai. Kuma nakan dunkule, wani lokacin in ce "La ilaha illallahu wahdahu lasharika lahu, lahul mulku walahul hamdu, wahuwa ala kulli shai'in kadir." In kin fadi wannan, kin yabi Allah, kin gode masa, kuma har yanzu kin girmama Shi a dunkule haka.

TAMBAYA: To Malam shi ne kirari ga Allah?

DAKTA YUSUF ALI: Yawwa shi ne kirari ga Allah kenan; kin gane ko? To sai kuma magana da kika yi cewa za a karanta Tabara ne kafin a yi barci ko lokacin da za a yi barci ko? Idan an ce lokacin barci sai mutum ya shirya gabaki daya, babu abin da zai yi illa barci. Saboda Nana A'isha (RA), kamar irin yadda Al-imamul Nawawi ya fada a cikin littafinsa Al-azkar, ya fadi wata Addu'a, ya ce Nana A'isha idan ana zazzaune a wurinta ba a fahimtar lokacin barcin ta ya yi sai an ji tana wannan addu'ar. To ashe kenan, addu'a ana karanta ta ne, wanda idan an karanta babu abin da za a sake yi illa a yi barci kawai. Sai mutum ya yi alwala ya zo ya kwanta, to sannan zai karanta "Tabaran." Kin gane ko?

To sannan kuma kan maganar cewa kangararrun yara kuwa, abin da muka ce shi ne "Ayatul kursiyyu" 313, salatul tunajjina kafa 1000, kulhuwallahu 1001, sai a tofa cikin tufan da yake sawa.

Har yanzu wadanda suka karbi istihara wacce ake karantawa don a ga wani abu, shi ma an ce bayan an idar da sallah ne. Shi kuma hadisi ne daga Sayyidina Ali (Karramal lahu wajhahu). Shi ma ya ce bayan an idar da sallah shi ma ana yaba ma Allah, ana gode wa Allah; to wannan dai ga wanda bai ji ba, to ga shi nan na fada yanzu irin yadda ake gode wa Allah da yadda ake yaba masa.

TAMBAYA: Daga Abubakar daga Fagge ta kudu. Ina yiwa Malam barka da zuwa wannan fili mai matukar farin jini ga al'ummar Manzo (S). Tambayata ita ce; wato muna aiki ne da wani mutumin Indiya, yana da gunkin da yake bautawa a kasarsu, kuma a cikin kamfaninsa nake aiki, to meye matsayina da shi?

DAKTA YUSUF ALI: Matsayinka da shi "lakum dinukum waliyadin." E, wato abin da Allah (T) yake bayyana mana shi ne cewa kada mumini ya riki kafiri majibincin lamarinsa. Wanda duk ya yi wannan, to babu wani abu nasa wajen Allah. Kamar a ce ko na lada ko na alkawarin zai masa gafara ko zai saka shi a Aljanna.

MAI GABATARWA: Malam akwai wata tambaya makamanciyar wadda ta gabata. Wani mutum ne ya rubuto ta ga wannan fili, inda yake cewa ya yi mu'amala da wani mutum sai daga baya kuma ya samu wannan mutum da ya yi mu'amala da shi wani Shugaba ne na ofishin yin caca. Shi ne yake tambaya, shin ya halatta ya ci gaba da mu'amala da shi ko ko ya janye jikinsa?

DAKTA YUSUF ALI: Ai bai halatta yin mu'amala da mutumin da ya kasance ke yin caca ba. Saboda caca nassinta ya zo a cikin al-Kur'ani saboda haka dukiyar da za a samu ta hanyar caca haramun ce. Bai kamata mutum kuma ya yardar ma kansa cin haramun ba. Sai idan ya kasance akwai lalura daga wannan, kuma Allah (SWA) ya ce, "innama yuridu shaidanu an yuki'a bainakumul adawata wal bagada fil khamri wal maisiri wa yasuddakum an zikirillah wa'anil salat…" Abubuwa guda hudu sune abin da Shaidan yake nufi ga masu caca da shan giya. Ya hada dai gaba, ya hana su sallah, ya kuma hana su zikiri. Wannan shi ne dalilin da ya sa ma aka hana caca. Za ta hana ka sallah kuma ta hana ka zikiri. Zikirin nan wanda wadansu ke ganin ba ma lallai bane. To amma ga shi Allah (SWA) ya hana wadannan abubuwa, illarsa shi ne zai hana ka zikiri da sallah, ko ya kawo gaba tsakaninku.

To kenan ashe cin irin wannan kudin haramun ne. Saboda Annabi (SAW) ya ce wanda yake ta'ammuli da dukiyar haramun, in ya ba ka haramun din kuma ba ka sani ba ka ci, wannan zai iya hana Allah ya karbi addu'arka, zai iya hana Allah ya karbi ibadarka ma. Saboda Manzon Allah ya ambaci wani mutum ya taho yana addu'a yana cewa, "ya rabbi, ya Rabbi, ya Rabbi mada'amahu haramun, malbasahu haramun, wamashrabahu haramun, waguziya bil haramun…" kuma an ciyar da shi ma haramun, yaya za a karba masa? Sai ka yi ta kokari ka tuba na irin abubuwan da ka ci a can baya. Kuma ka yi kokarin neman aiki har Allah (T) ya sa ka samu wani aiki daban, ka bar wannan din.

TAMBAYA: Daga wata daliba daga Jakara. To Malam mun gode fa, muna godiya, Allah (T) ya saka maka da alherinsa. Don Allah Malam ina neman wata fatawa ne saboda yara da farin jini da kuma karatu, kuma ina da wata kanwa tawa da mijinta kodayaushe sai rigima tsakaninsu, ya rika yi mata fada babu dalili da cin mutunci, kuma iyayenmu daya da shi, mu 'yan uwan juna ne, shi ne muke son addu'a.

DAKTA YUSUF ALI: To da farko dai abin da ya shafi fahami na farin jini ita mace tana bukatar abubuwa guda biyu. Alal misali ta samu farin jinin kuma sannan ta samu miji. Wato za ka ga tana da farin jinin, amma kuma mijin bai tsaya ba, alal misali. To abin dai da ya shafi farin jini gaba daya jimla, akwai ayoyi a cikin al-Kur'ani wadanda ake rubutawa ake sha. Akwai "Zuyyina lin nasi hubbu shahawat…" har dai ya zuwa karshen wannan izu din, wato aya ce fa guda daya (3:13). Sannan akwai irin su "wa alkaitu alaika mahabbatan minni…"(20:37) . Akwai "Wa zayyannaha lin nazirin…"(15:15). Akwai "ya ayyuhal lazina amanu latakunu kallazina azau Musa fabarra'ahullhu mimma kalu wakana indallahi wajiha.." (33:47) Akwai kuma "falamma ra'ainahu akbarnahu wakadda'ana aidiyahunna.."(12:30) har dai izuwa karshen ayar. Akwai "walakad hammatbihi wa hamma biha.." (12:33) Akwai "…wal kaziminal gaiza wal afina aninnasi wallahu yuhibbul muhsinin." (3:133). Akwai "awaman kana maitan fa'ahayaynahu waja alna lahu nuran yamshi bihi finnasi kaman masaluhu fiz zulumati laisa bi kharijin minha, kazalika zuyyina lillakafirina ma kanu ya'amalun." (6:121) Akwai kuma "kulid ullah awid urrahman ayyamma tad'u falahul asma ulhusna.." (17:109) har izuwa karshen sura ta Isra'i. Wadannan gaba daya a jumlace sune. Akwai "alamnashraha," akwai kuma "asallahu anyaj'ala bainakum wa bainal lazina adaitum minhum wawadda." (60:6). Wadannan sune ayoyin da suke cikin Kur'ani gaba daya, wadanda malamai wani ya fadi daya, wani ya fadi biyu, wani ya fadi uku, to ga shi nan duk na fado su gaba daya. Sune wadanda suke da farin jini sune na kwarjini, sune na kabuli. Mace tana iya rubuta wannan kafa dubu ko kafa dari alal misali, gwargwadon dai irin abin da take nema da kuma gwargwadon ikonta. Idan miji aka samu, to ana iya rubuta "walakad hammat bihi…" ita kadai guda dubu, to insha Allahu mijin zai tsaya. To wannan shi ne abin da ya shafi farin jini.

Kuma abin da ya shafi na neman miji ga shi nan ana rubutawa. To akwai abubuwa da dama kamar irin su ayoyi na sulhu. Akwai kuma na samun tausasawa na miji, to idan ya kasance mijin nan mai fada ne, ana jin tsoron zai zalunci wani, zai yi waye da waye, zai yi duka ko zai zagi, to akwai "Akwai "…wal kaziminal gaiza wal afina aninnasi wallahu yuhibbul muhsinin." (3:133). Akwai "wa iza fa'alu fahishatan au zalamu anfusahum zakarullaha fastagfaru lizunubihim, waman yagfiruz zunuba illallah.." (3:134) wato dai har izuwa "wani'ima ajarul amilin." Ayoyi ne sun kai wajen guda hudu da suke cikin "Lantanalul birra." To wadannan ayoyi sune ake rubuta su ranar Juma'a da daddare, to sai ya kasance wacce take jin tsoro, ko kuma shi wannan mutumin a ba shi ya sha. To za ka ga zuciyarsa ta yi sanyi.

Ko kuma ka rubuta wadannan ayoyi ka rike, to insha Allahu ba zai cuce ka da komai ba. Kuma har yanzu daren Juma'a idan shabiyun dare ya gota, nan kuma malamai ba daya ba, wannan barkatai a cikin littattafan malamai cewa akwai hanya guda biyu, mutum idan ya kasance akwai wani mutum da yake jin tsoron kinbarsa, wato ba sa shiri suna sabawa, shi kuma yana so ya ci gaba da zama da wannan mutumin, to shi kenan zai iya yin salla raka'a biyu sannan ya karanta "Lakadja'akum," kafa talatin, sannan ya ce "Allahumma ya Rabbi anta hazbi ala fulanin …" ya fadi haka sau daya, a wannan kauli kenan, insha Allahu in ya fadi wannan, Allah (T) zai tausasa zuciyar wannan ya sa masa rahama da tausayi. Akwai hanya ta biyu shi ne dukkaninsu, a'a ba "Lakad ja'akum" gaba daya za a karanta ba, a'a "fa intawallau fakul hasbiyallahu la'ilaha illahuwa alaihi tawakkaltu wahuwa rabbul arshil azim" "Allahumma anta hazbi ala.." sai ka fadi sunan mutumin (ka karasa addu'ar), to nan za a yi kafa talatin wannan zai iya yi har dari, amma fa daren Juma'a wato ranar Alhamis da daddare bayan sha biyu ta wuce ake yin wannan. Wannan yana da mamaki kwarai da gaske wajen samun taushi da kuma samun daidaituwar zama tsakanin wadanda ba sa shiri, ko maza ne ko tsakanin miji da mata ne, wannan kuma wata hulda ce daban.

TAMBAYA: Wata daliba ce daga Sharada. Malam tambayata ita ce kullum idan dare ya yi, da an ce karfe takwas ta yi ko tara, sai barci ya rufe ni, kaina sai ya kama ciwo. Nakan so na tashi in yi sallah irin kiyamullailin nan, to ba zan iya ba, duk sai jikina ya kama yi mini ciwo, shi ne tambayata ta farko. Ta biyu kuma, Malam ciwo ne haka a kafata, in ya tashi sai ya rinka daddaye fatar kafata.

DAKTA YUSUF ALI: To da farko maganar barci akwai addu'o'i wadanda ake yi don barci, kodayake ba wai barcin ne ba kya samu ba, a'a barcin ne yake yin yawa. Abin da za ki yi shi ne akwai wasu ayoyi da suke cikin suratul A'araf "Inna rabbakumullahul lazi khalakas samawati wal arda fi sittati ayyamin summastawa alal arshi, yugshillailan nahara yadlibuhu hasisan wasshamsa wal kamara wannujuma musakkaratin bi amrihi, ala lahul khalku wal amru tabarakallahu rabbul alamin. Ud'u rabbakum tadarru'an wakhfya innahu layuhibbul mu'utadin. Wala tufsidu filardi ba'ada islahiha wad'uhu khaufan wadama'an inna rahmatallahi karibun minal muhsinin." (7:53) Sune ake karantawa kafa uku in za ki kwanta barci, insha allahu barcin ba zai zo ya dame ki ba.

Sai maganar ciwon kafa. Akwai ciwon kafa, to da akwai abubuwa kamar guda biyu. Akwai wani ciwo da ake cewa dahis. Akwai wanda ake cewa nikes, wadannan duk wadansu ciwuka ne wadanda sukan faru a kafa da hannaye. Kuma shi nikes ana ganin cuta ce ta masu jin dadi, galibi a saboda cin abubuwa masu maiko da sauransu da masu gina jiki, to su suke irin wannan cututtuka. Mukan ba da addu'o'i, to amma kuma akwai wanda muke hadawa. Su wadanda muke hadawa, su wadannan ba mu cika fadarsu sosai da sosai ba, abubuwa ne da suka shafi itatuwa da hade-hade haka. Amma dai abin da muke fada ko yau shi irin wannan akwai wadansu ayoyi guda biyu cikin al-Kur'ani, wadanda duk sun hade haruffan da aka rubuta Kur'ani da su, huruful hija'iyya. Wato na farko akwai "summa anzala alaikum min ba'adi gamman amnatan nu'asan yagsha da'ifatan minkum" har ya zuwa "alimun bi zatissudur." Aya ce sananniya da take cikin Ali Imran. Ta biyu kuma tana cikin izu goma wajen karshe ko kuma a "Lakad radiya" ko "Muhammadur rasulullah.." wato kenan a cikin suratul Fatahi kenan. "wallazina ma'ahu ashidda'u alal kuffari ruhama'u bainahum.." har izuwa karshe. Wadannan ayoyi guda biyu sun hado haruffan da aka rubuta al-Kur'ani gaba daya, wato sune harafi guda ashirin da takwas. To idan ya kasance aka rubuta wadannan ayoyi aka wanke da man zaitun tana shafawa tana shan cokali daya, safe da yamma, insha Allah za ta ga wannan ciwon kafa din ya warke, da duk wani ciwo wanda yake jikinta a duk inda yake a jiki, shi ma insha Allah.

Za mu ci gaba insha Allahu a mako na gaba.

Komawa babban shafinmu                   Komawa saman wannan shafin