Shafin Dakta Yusuf Ali

Bismillahir rahmanir rahim

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai
Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata Ga Annabi Muhammmadu Da Tsarkakan Mutanen Gidansa



Annabi (s) Ya ce, Ranaku da darare ba za su kare ba har sai Allah Ya tasar da wani mutum cikin Ahlulbaitina sunansa kamar sunana, zai cika kasa (duniya) da adalci kamar yadda aka cika ta da zalunci                 Ustaz Yusuf Ali 
ZA MU RIKA CANZA SHAFIN NAN A KOWACE LAHADI.    Ranar karshe da muka canza: 13 ga Yuli, 2004

Abubuwan Da Ke Ciki

Ihya'us sunna

TAMBAYA TA 1
Assalamu alaikum. Muhammad Awwal Sharif ne daga Zariya ke magana.

Ina yi wa Shehi barka da zuwa. Kuma ina yi wa Shehu bangajiya na hidimomin da aka yi, ina kuma kara wa Shehi addu'a, Allah Ya kara wa Shehi martaba da daukaka. Ya kara kiyaye mu, Ya kara kiyaye Shehi. Allah Ya kara masa karama. Akwai tambayar da nake da ita guda daya, amma tambayar tawa shi ba a bangaren ilimi bane, a kan bangaren tarihin Shehi ne. Kwanakin baya can na karanta a wata jarida ALMIZAN, cewa Shehi sun yi karatu ne da Malam Ibrahim Al-Zakzaky na nan Zariya, ko sun zauna tare ne, to shi ne ban gane ba? Shi ya sa na ce in na bugo zan tambayi Shehi a kan dangatar sa da shi Malam din? Daga karshe kuma ina kara ma Shehi addu'a dai, ya kara hakura da jama'a, wannan martaba da aka samu, dole wanda ya samu martaba irin ta Shehi sai ya samu irin wannan. Tunda Manzon Allah (S) yana cewa, "Ashaddun nasa bala'an…" Saboda haka dole Shehi ya yi ta samun irin wannan jarrabawa, irin wannan, na wajen mutane, na wasu maganganu. WalLahi ba komai bane illa daukaka ce da kuma martaba. Kuma almajirai mun sani, kuma muna alfahari da shi, a kan wannan abin da ya yi mana. Allah Ya kara daukaka shi. To, Shehi mu biyu ne, akwai wani Aminina da yake shi ma yana wahalar samun layin, Malam Hamisu yana da sako. Ga shi: Malam ni dai ina neman barar du'a'i na neman Allah Ya yi min budi. A huta lafiya.

TAMBAYA TA 2
Assalamu alaikum. Alhaji Mustafa ne. AkramakalLah, kafin na yi tambaya zan fara da abin da filin ya bude da shi a yau na godiya da wannan abu da na ji ya faru a filin kaddamar da wannan littafi na Mai martaba Sarki. Kuma Allah ya kara daukaka ka, Allah kuma Ya kara bayyana sirrinka a duniya, wadanda ba su fahimce ka ba su fahimce ka, kuma shi kansa Mai martaba, muna taya shi murna da wannan abu, Ya kara ja mana ransa cikin imani da lafiya. Abu na farko, a cikin karatunka na jiya akwai bayanin da ka yi na karanta "La'uksimu bi hazal balad.." ban dai fahimci yadda abin yake ba, to shi ne nake neman Malam ya kara bayani. Na biyu, Malam akwai wani bawan Allah da ya ce da akwai wani da ya daukar wa kansa alkawari tun wajen shekara biyu da suka uce haka, duk bayan sallar Magariba zai karanta Alamnashraha, ina zaton 41 ya ce, shi ne yake so Malam ya dan kara masa bayani game da ita wannan aba.


TAMBAYA TA 3
Assalamu alaikum. Alhaji Hamisu Tata, kofar Wambai ne. Amma zama ya dawo da ni nan Tukuntawa. Na dade ina sauraron Malam. Kullun ina 'trying' na sami layin sai ya zamana ban samu ba, yau dai Allah ya sa na samu, saboda haka za mu gaisa da Malam.


TAMBAYATA 4
Muhammad ne yake magana. Malam ina da tambayoyi guda biyu. Da farko ina so in san hukuncin abin da aka shuka, wato yabanya da ta isa minzalin da za a girbe shi. Sannan kuma wata fa'ida nake so a tunatar da ni. Akwai wata aya cikin suratul Yasin, "waja'alna min baini aidihim saddan wa min khalfihim saddan, fa agashainahum fahum la yabsirun." Akwai lokacin da mahaifina ya kasance ya samu rashin lafiya, ta shanyewar rabin jiki, to wani Malami ya zo ya ba mu fa'idar na bayan sallar Isha, mu karanta masa masa wani adadi, muna tofawa a bangaren da ya shanye daga jikinsa. To wannan adadin ne na neme shi na rasa, kuma mun ga tasirin abin. To insha Allah, da yardar Allah na san Malam ba ya kasa sanin wannan al'amari, muna so ya tunatar da mu.


TAMBAYA TA 5
Malam Awwal ne daga Goron Dutse. Malam tambayar da nake da ita, akwai wani abokina da muke tare da shi, to a kan harkar da nake zan yi tambaya a kai. Akan dan sami kudi haka, kamar jabu guda daya zuwa guda biyu a cikin kudi, nakan bashi shawara wani lokacin daga yayin da suka zo hannunmu mu yaga su, sai ya ce, a'a tunda ba shi ya yi ba, ba shi ya sako ba, shi ba zai yarda da haka ba. Wani lokacin nakan yi nasara da shi a kan haka, wani lokacin yakan ki yarda. Shi kenan sai na gamu da shi, to yau dai muka dan tattauna da shi. Shi ne yake cewa, shi a ina ne nake nuna masa cewa yayin da suka zo hannunmu, idan muka bar su suka ci gaba, nake ga daga nan za mu yi daukar wani nauyi daga cikin wadanda suka shirya wadannan abubuwa. Sai yake nuna min bai yarda ba, shi ne na ce masa to ya saurare ni, in Allah Ya yarda zan kara neman fatawa a kan irin gyaran da na masa.


TAMBAYA TA 6
Sani Babaje ke magana. Malam ina da tambaya, a, kasancewar zamani yanzu, kusan Allah Ya sa ilimi ya yi yawa, wasu abubuwa duk da haka suke iya ilimi na da yanzu sun canza, wato kuma yanzu akan yo musaya, ko kuma aro daga sauran mazhabobi a yi amfani da su. Alal misali da kamar yadda muka sani, idan mutum yana bin mai Liman salla, in Azahar yake yi, liman ma Azahar yake yi, haka Magariba da sauransu, in kuma nafila yake to shi ma nafila yake. To amma yanzu, kusan abin ya ragu ba haka ba, sai ya zamana za ka ga wasu mutanen ka aje mutum ma ko kara'i yake ma, wannan kuma ba kara'i yake ba, ko kuma wani mutum ya samu salla da liman, ya samu kamar raka'a biyu, yana cikin cike tasa biyun, sai wani kuma ya zo ya damfara da shi, shi ma ya jona, ko kuma kamar zai sallar farilla, bai samu jam'i ba, sai wani ya zo ya yi nafila raka'a biyu, sai shi ma ya yi, duk wadannan abubuwa ga wanda bai sani ba zai ga kamar wasu abubuwa daban, amma ga mai hankali, ya san cewa da wuya a ce mutum ya yi wannan ba tare da hujja ba. Shi ne nake so ko Malam zai yi bayanin hujjoji na yin wadannan abubuwa.


 

Al'amurran Yau Da Kullum

Daliban da suka sauke Alkur'ani a gaban Wamban Kano, Abbas Sunusi, kusa da shi kuma Ustaz Yusuf Ali ne(hagu)
Nada Ustaz Yusuf Ali Darakta ya dace


Daga Ali Kakaki

Sarkin Kano, Alhaji Dakta Ado Bayero ya bayyana nadin da aka yi wa Ustaz Dakta Yusuf Ali a matsayin Darakta mai binciken yadda Alkalan kotunan shari'ar Musulunci na Jihar Kano suke gudanar da shari'o'insu a matsayin abin da ya cancanta kuma ya dace kwarai da gaske.

Da yake jawabi a madadin Mai martaba Sarkin, Ciroman Gwale, kuma babban dan Sarkin na Kano, ya ce ya je ofishin Daraktan ne Ustaz Yusuf Ali da ke harabar Ma'aikatar shari'a ta jiha a Audu Bako Sakateriya Kofar Nasarawa domin cika umurnin Mai martaba Sarki da ya umurce shi da ya zo ya isar da wannan sako na nuna dacewa da nadin Ustaz din a wannan matsayin na Darakta.
Ci gaban labarin


Ihya'us Sunna ta yi bikin saukar karatu

Daga Ali Kakaki

A ranar Talata 27/3/1424 ne, makarantar Madrasatul Ihya'us Sunna, da ke unguwar Tudun Maliki Kano, ta yi gagarumin bikin saukar karatun Alkur'ani mai girma karo na farko wanda aka gudanar da shi a harabar masallacin Shaikh Dakta Yusuf Ali.

Wakilinmu, wanda ya samu halartar bikin saukar karatun, ya shaida mana cewa; dalibai mata guda uku ne na makarantar suka sauke Alkur'ani, sai namiji guda daya, wanda Allah (T) ya ba shi ikon haddace Alkur'ani, mai suna Ahmad Yusuf Ali.
Ci gaban labarin


Tarihin rayuwar Ustaz Dakta Yusuf Ali

A ranar Juma'a 29 ga Jimada Sani, 1423, (6 ga Satumba, 2004) Aliyu Yusuf Kakaki ya tattauna da fitaccen Shehin Malamin nan da ke Kano, Shaikh, Ustaz, Dakta, Yusuf Ali, wanda ya sha gaban Malumma da dama a Afrika gaba daya wajen yada addinin Allah (T) da isar da sakon Manzon Allah, Muhammad (SAW) ta kafafen yada labarai, babu dare babu rana.

Cikin tattaunawar Shaikh Yusuf Ali ya bayyana tarihinsa tun daga shekarar da aka haife shi da garin da aka haife shi, karatunsa na addini da na zamani, ayyukan da ya taba yi, kafafen yada labaran da yake yada karatuttuka cikinsu, yawan wakokinsa, kudaden da yake kashewa wajen biyan kafafen yada labaru da babban burinsa. Ci gaban hirar



                          

Sauran Abubuwa

ILIMI KOGI NE

Filin Ilimi Kogi Ne
Da aka buga a jaridar DILLALIYA ta 42

Wasu Shafuffukan Musulunci
. Shafin Kungiyar Jannah
.
Shafin Kungiyar Sunnah
.
Shafin Naqashabandiyya
.
Shafin Al-islam  
.
Hizbullah Labanon  
.
Shafin Kungiyar Islamic Awareness
Gaya wa aboki
Rubuta suna:

Rubuta e-mail:

Rubuta e-mail na aboki:

Ra'ayinka:

Naka kwafin: 



Ka rubuto mana wasika ta wannan adireshin