Ilimi Kogi Ne Filin Shirin asmsa tambayoyin masu sauraron daga Ustaz Yusuf Ali

Filin amsa tambayoyin masu saurare daga Ustaz Yusuf Ali
Lahadi 22 Rabi'us Sani, 1424                



 Maigida da Uwargida | TAMABAYA TA 1  | TAMBAYA TA 2 | TAMBAYA TA 3 | TAMBAYA TA 4 | TAMBAYA TA 5 | TAMBAYA TA 6 | TAMBAYA TA 7 
Ilimi Kogi Ne | TAMBAYA TA 8
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
Ilimi Kogi Ne:

Mai karatu wannan shi ne filin Ilimi Kogi da Ustaz Yusuf Ali ya yi ranar 17 ga Agustan 2002.

Tambaya ta 3

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Alhaji Hamisu Tata, kofar Wambai ne. Amma zama ya dawo da ni nan Tukuntawa. Na dade ina sauraron Malam. Kullun ina 'trying' na sami layin sai ya zamana ban samu ba, yau dai Allah ya sa na samu, saboda haka za mu gaisa da Malam.

DAKTA YUSUF ALI: Madalla.

ALHAJI HAMISU TATA: Allah Ya gafarta Malam.

DAKTA YUSUF ALI: Assalamu alaikum.

ALHAJI HAMISU TATA: Ya almajirai?

DAKTA YUSUF ALI: Lafiya kalau.

ALHAJI HAMISU TATA: Allah Ya kara abin da yake da akwai.

DAKTA YUSUF ALI: Amin.

ALHAJI HAMISU TATA: Sai dai ga shi akwai mahassada, kullum muna fama da su. Amma ba wani abu. Mun san Ma'aiki (S) ya ce, "kullu ni'imatun mahasudatin." To mu mun san irin aikin Malam, kuma alhamdu lilLahi, kullum ana dada wayar da kan jama'a. Sai dai mu yi fatan Malam ya dada hakuri. Allah Ya saka da alheri, in Allah ya yarda za a dinga jin mu a kai, a kai.

MAI GABATARWA: To mun gode. Malam wannan ka ga bayani ne mai gamsarwa sosai. Da ma wannan haka yake, ai kamar jihadi yake.

DAKTA YUSUF ALI: To don haka duk wani hassada ba komai bane. Allah ma an yi masa, Manzon Allah (S), duk Annabawa an yi masu. Duk waliyyan Allah wadanda suka fi mu su ma an yi masu. To kuma duk wanda ya ce dama zai taka wannan kalamin haka ne. Idan da ba don hassada ba, ai da duk duniya duk musulmi ne. Ka dubi matsayin Manzon Allah, ka dubi fa Allah Ya ce, "innaddina indallahil Islam." Allah ba shi da wani addini sai Musulunci. "Wamay yabtagi gairil islama dinan falay yukbalu minhu." Wanda duk ya ce zai nemi wani addini ba Musulunci ba, to ba za amsa masa ba. "Wa huwa fil akhirati minal khasirin." Ko? Amma duk da haka, to Musuluncin na Allah ya gama halittunsa gaba daya? Halittar ta Allah ce, amma sun ki, gaba suke da shi. Gaggaya mana maganganu suke.

Komawa babban shafinmu                   Komawa saman wannan shafin