Ilimi Kogi Ne Filin Shirin asmsa tambayoyin masu sauraron daga Ustaz Yusuf Ali

Filin amsa tambayoyin masu saurare daga Ustaz Yusuf Ali
Lahadi 22 Rabi'us Sani, 1424                



 Maigida da Uwargida | TAMABAYA TA 1  | TAMBAYA TA 2 | TAMBAYA TA 3 | TAMBAYA TA 4 | TAMBAYA TA 5 | TAMBAYA TA 6 | TAMBAYA TA 7 
Ilimi Kogi Ne | TAMBAYA TA 8
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
Ilimi Kogi Ne:

Mai karatu wannan shi ne filin Ilimi Kogi da Ustaz Yusuf Ali ya yi ranar 17 ga Agustan 2002.

Tambaya ta 2

Assalamu alaikum. Alhaji Mustafa ne. AkramakalLah, kafin na yi tambaya zan fara da abin da filin ya bude da shi a yau na godiya da wannan abu da na ji ya faru a filin kaddamar da wannan littafi na Mai martaba Sarki. Kuma Allah ya kara daukaka ka, Allah kuma Ya kara bayyana sirrinka a duniya, wadanda ba su fahimce ka ba su fahimce ka, kuma shi kansa Mai martaba, muna taya shi murna da wannan abu, Ya kara ja mana ransa cikin imani da lafiya. Abu na farko, a cikin karatunka na jiya akwai bayanin da ka yi na karanta "La'uksimu bi hazal balad.." ban dai fahimci yadda abin yake ba, to shi ne nake neman Malam ya kara bayani. Na biyu, Malam akwai wani bawan Allah da ya ce da akwai wani da ya daukar wa kansa alkawari tun wajen shekara biyu da suka uce haka, duk bayan sallar Magariba zai karanta Alamnashraha, ina zaton 41 ya ce, shi ne yake so Malam ya dan kara masa bayani game da ita wannan aba.

DAKTAYUSUF ALI: To, to ita dai suratul Baladi lokacin da muke karatu ne, to galibi wadansu abubuwan suna da yawan gaske, fa'idojin nata suna da yawa, kuma na fadi abubuwa a game da ita. To, ba shakka akwai na maganar za a karanta, kuma a rubuta a kyalle. Kyallen nan ana iya laya da shi, ko kuma a cikin wani abu kamar a rubuta a sha. Na wanda za a rubuta a kyalle shi ne dai muka fada. Kuma ana iya rubutawa ne kafa daya,kawai. To saboda haka mun yi sauran bayanai. Ka san kowane muhalli da akwai abubuwan da suke zuwa sannan. Sai ka ce kaza, to amma dukkan abubuwan da aka ji an fada suna nan a rubuce, idan yana bukatar su akwai su a rubuce, ko kuma ina ga duk sad da zan fito yawanci sai na rubuta wadannan abubuwan ma tukuna. Kafin na fade su sai na rubuta, ko da da wani mai so, maimakon a tsaya ana ta kara karanto masa, to sai a ba shi, sai ya kwafa.

Ita ko Alamnashraha, ana yin dai salla ne raka'a biyu, wato dai kowace irin bukata da mutuma yake da ita, musamman a yayin da mutum ya kasance, ya yi ta neman bukatu iri-iri, kuma ya jarraba lakankuna iri-iri. Kuma ya yi wadansu dai dabaru iri-iri, wanda yake ganin bukatar za ta biya, ba ta biya ba, to a sannan ne ake amfani da ita Alamnasharaha adadin jumlatarta shi ne 152. To idan ya kasance, mutum bayan ya yi salla raka'a biyu, Fatiha kafa daya da kuma Inna anzalnahu, ta biyu Fatiha da Izazul, to bayan sallama sai mutum karanta Alamnashraha 152. To insha Allah wannan bukatar da ta wahala bai same ta ba, wanda ya kuma jarraba lakunkuna da dabaru amma duk ba su yi ba, to insha Allah Allah zai warware.

To kuma har yanzu akwai wani sirri, wanda kuma daga baya amma na ga malamai sun fada, amma wannan ni Allah Ya sanar da ni kawai. An kawo wani yaro ne, yaron kuma ina jin dan masu hali ne, sai aka dauke ni aka kai ni gidan, in yi masa magani. Ina jin tun wajen shekarun saba'inoni ne, don kusan ina can Galadanci, a nan gidan Danlawan. To a wannan lokacin ne ya kasance sai kawai da aka kai ni, ana ta labarina ne, sai aka dauko ni in yi wa wannan yaro magani. Sai na karanta "Alamnashraha laka sadarak," zuwa "innama'al usuri yusura," kafa bakwai, in tofa masa. Na kuma karata "KulhuwalLahu biyar, shi kenan kawai sai ya tashi. Mutane ma ba su fashe ba, masu zuwa dubiya da koke-koke, sai ga shi har ya dau keke ma har ya fita. To saboda haka tun daga wannan lokacin fa kowace irin cuta a wannan lokacin in dai na karanta "Alamnashraha," zuwa "Innama'alusri yusra," kafa bakwai, to sai ka ga cewa an samu biyan bukata. Kuma da wannan "KulhuwalLahu," biyar. Saboda haka tunda dai ya ce yana neman lakani, to ga shi nan an ba shi.

Komawa babban shafinmu                   Komawa saman wannan shafin