Ilimi Kogi Ne Filin Shirin asmsa tambayoyin masu sauraron daga Ustaz Yusuf Ali

Filin amsa tambayoyin masu saurare daga Ustaz Yusuf Ali
Lahadi 22 Rabi'us Sani, 1424                



 Maigida da Uwargida | TAMABAYA TA 1  | TAMBAYA TA 2 | TAMBAYA TA 3 | TAMBAYA TA 4 | TAMBAYA TA 5 | TAMBAYA TA 6 | TAMBAYA TA 7 
Ilimi Kogi Ne | TAMBAYA TA 8
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
Ilimi Kogi Ne:

Mai karatu wannan shi ne filin Ilimi Kogi da Ustaz Yusuf Ali ya yi ranar 17 ga Agustan 2002.

Tambaya ta 4

TAMBAYA: Muhammad ne yake magana. Malam ina da tambayoyi guda biyu. Da farko ina so in san hukuncin abin da aka shuka, wato yabanya da ta isa minzalin da za a girbe shi. Sannan kuma wata fa'ida nake so a tunatar da ni. Akwai wata aya cikin suratul Yasin, "waja'alna min baini aidihim saddan wa min khalfihim saddan, fa agashainahum fahum la yabsirun." Akwai lokacin da mahaifina ya kasance ya samu rashin lafiya, ta shanyewar rabin jiki, to wani Malami ya zo ya ba mu fa'idar na bayan sallar Isha, mu karanta masa masa wani adadi, muna tofawa a bangaren da ya shanye daga jikinsa. To wannan adadin ne na neme shi na rasa, kuma mun ga tasirin abin. To insha Allah, da yardar Allah na san Malam ba ya kasa sanin wannan al'amari, muna so ya tunatar da mu.

DAKTA YUSUF ALI: To maganar yabanya ko? In mutum bai san yabanya ba, shi ne kamar a yi shuka ta fito, walau gyero ne ko dawa ce ko masara ce ko gyada ce ko gurjiya ce, amma kafin a ce ta kai minzalin ta kai ta fitar da kai ko ta fara 'ya'ya, kuma har ta nuna a ci, a sayar.

To a musulunce sai da yabanya, ita yabanyar kanta, in akwai wata bukatar ta yin haka, idan aka dubi usuli na shari'a, ba za a ce a'a ba, ko kuma a ce haramun ne ba, matukar dai cewa, wato sun hadu a kan sharadinsu. Shi ai addinin Musulunci ai kodayaushe akwai wadansu ka'idoji. Alal misali kamar "al musulimuna ala shurudihim, illa shardan yuharrimu halalan aw yuhallilu haraman." Kuma "kullu shardun laisa fi kitabilLah wa huwa badilu wa lau kana alfasanat." Wato kodayaushe idan matsala ta zo, to sai ka dauki irin wadannan ma'aunai, ka auna da su. To matukar dai cewa musulmi suka shardanta, wato sun saka wata ka'ida a junansu, kuma har yanzu "antaradun minhum" "la darara wala dalala;" da yarda tsakaninsu, ba cuta ba cutarwa. Suka ce za su yi cinikin wannan yabanya, da lura da tunanin abin da idan yabanyan nan ta girma zai kasance a samu, da kuma kula da mai yiwuwa a samu fari, mai yiwuwa wani abu ya zo ko daga Allah, ko wata iska, ko wata kankara ta zo ta ta lalata wannan, da kuma lura da irin yadda mai yiwuwa ko abin da ake tsammani zai zama haka ko ko ba haka ba, to idan ya kasance aka zo aka yi da yarjejeniya, kodayake ta wani bangaren za ka ga kamar ba wai ana nufin cewa a'a amfanin ake sayarwa ba, a'a yabanyar ce za a sayar. Ka ga shi ne ya sa aka ce ai an hana cinikin kamar 'ya'yan itace, "kabala an yabduwa salahu," kafin ya nuna. To ka ga nan maganar 'ya'yan ake yi, akwai garari.'Ya'yan aka saya wanda za a zo a debe, daga baya kuma a sayar, amma wannan yabanya ce, ake magana. Saboda haka yabanya za a saya, kuma abin da ya faru, karuwa abin ya yi, ga yadda ake zato ko raguwa ya yi, ka ga wannan kuma a kan matukar an yi sharadi cewa duk abin da fa ya zo daga baya ko karuwa ko raguwa naka ne, kai mai saye, aka yarda a haka, shaidu suka tabbatar, ka ga wannan babu zancen garari a ciki, an san abin da aka saya. WalLahu a'alamu, wannan shi ne abin da nake gani.

Yanzu da za a ce ka kirga wadannan haruffai "waja'alna mini aidihin siddan wa min khaifin siddan fa agshainahum fahum la yubsiruna" wato zan ba ku ma wato ka'ida gaba daya, shin ta yaya ake ganewa wato a saka wa addu'a, ko a saka wa wani abu lakani, wato adadi, kafa kaza? Akan dubi abubuwa wadanda Allah (T) Yake amfani da su, ko dai bakwai, Yana da sammai bakwai, kassai bakwai, a, siradi bakwai, kofar Aljanna bakwai, kofar wuta bakwai, me ya sa? Lallai a wannan adadi akwai sirri. To saboda haka duk abin da ka dauka ka karanta bakwai, ko ka yi sau bakwai, to insha Allah za ka samu biyan bukata, saboda idan da ba shi da wani sirri, to babu wani abin da zai sa Allah Ya sa wannan.

To haka nan kuma ana karanta 41, ko 40. To za ka ga cewa Annabi Musa (AS) Allah (T) Ya fadi, "Mikati Rabbihi arba'ina laila" kwana arba'in. Ko kuma "salasila laila, wa atmamnaha bihi ashara fa tamma arba'ina laila." Sai aka ce, to akwai sirri. Me ya sa ba ashirin ba? Me ya sa ba hamsin ba? To haka nan. To sannan kuma wadannan harufai in ka dube su yanzu, da za ka kirga su za ka ga yawansu. Dazu mun ba da fa'idar Alamnasharaha. Alamnasharaha idan da za ka kirga yawan haruffan za ka ga cewa 152. To ka ga wannan shi ne ya zama shi ne adadinta, adadin haruffan ko sura ko wani suna ne ko kuma wata aya ce, to in ka kirga haruffan, to wannan shi ne suke bayarwa galibi da adadi. Ko kuma a'a kana iya buge su, 'wau' din nan ya zama shida ne, 'ja' ya zama uku, 'allikafa' ya zama saba'in, 'lanjaye' ya talatin (30), 'nun guda' ta zama hamsin (50), 'alif' ya zama daya, 'mimjaye' ya zama hamsin (40), 'nu'ara' ya zama ta zama hamsin (50), 'ba' ta zama biyu, baina din nan ko? 'ya' ta zama goma (10), 'na' ya zama hamsin (50). To da haka, da haka, har dai ka zo kan "siddan fa agshainahum fa hum layubsiruna" har inda za ka samu 'sin' din nan, 'sadi' ya zama dari uku (300), wato a (sharkiya" kenan ko kuma sittin a garbiyya, 'ra" ta zama dari biyu (200), shi kenan 'wau' ya zama shida, 'nu'ara' ta zama hamsin (50). To in ka tattara wannan ko da kakuleta ne, ko da wani abin, in ka tattara su, to adadin abin da ya ba ka shi ne adadinsu bil jamalil kabiri, da jamlarsa mafi girma kenan. To sannan kuma to wannan ya fi tasiri, ko kuma a'a, sai ka dubi adadil mursalin, adadin mursalai, adadin as'habu Dalut, adadin as'habu Badar. Musulmi 313 sun yi yaki da wadanda suka fi su karfi, su ka fi su komai na dabarar yaki, amma sun yi galaba. Meye adadinsu? 313.

Daluta ya yaki Jaluta, ya yi galaba da shi, su nawa ne? Su dari uku ne da goma uku. Manzanni wanda Allah (T) Ya ce, "Allahu yastafi minal mala'ikati rusulan wa minan nas." Allah Yana zabar wanda Ya ga dama Ya tashi daga mutane ko daga mala'iku ya mai da su Manzanni, duk yawan halittar nan gaba daya ta mutane, 313 kawai wannan adadin Allah Ya zaba. To lallai akwai sirri, saboda haka duk abin ka karanta 313 za ka samu biyan bukatarsa. To haka nan kuma suka ce "kul alifun, kuz alifun, kul alfa, kuz alfan, kul alfa," ma'ana "kuz alifun, kul alfa" ma'ana duk abin da ka dauka aya ce harafi ne, wata sura ce, ka karanta dubu (1000), to insha Allahu za ka samu biyan bukata, shi ne karshen adadinsa.

Komawa babban shafinmu                   Komawa saman wannan shafin