Tarihin Ustaz Filin Shirin asmsa tambayoyin masu sauraron daga Ustaz Yusuf Ali

Filin amsa tambayoyin masu saurare daga Ustaz Yusuf Ali
Lahadi 22 Rabi'us Sani, 1424                



 Maigida da Uwargida | TAMABAYA TA 1  | TAMBAYA TA 2 | TAMBAYA TA 3 | TAMBAYA TA 4 | TAMBAYA TA 5 | TAMBAYA TA 6 | TAMBAYA TA 7 
Ilimi Kogi Ne | TAMBAYA TA 8
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
Labarun Ustaz Yusuf Ali:

Tarihin rayuwar Ustaz Dakta Yusuf Ali

A ranar Juma'a 29 ga Jimada Sani, 1423, (6 ga Satumba, 2004) Aliyu Yusuf Kakaki ya tattauna da fitaccen Shehin Malamin nan da ke Kano, Shaikh, Ustaz, Dakta, Yusuf Ali, wanda ya sha gaban Malumma da dama a Afrika gaba daya wajen yada addinin Allah (T) da isar da sakon Manzon Allah, Muhammad (SAW) ta kafafen yada labarai, babu dare babu rana.

Cikin tattaunawar Shaikh Yusuf Ali ya bayyana tarihinsa tun daga shekarar da aka haife shi da garin da aka haife shi, karatunsa na addini da na zamani, ayyukan da ya taba yi, kafafen yada labaran da yake yada karatuttuka cikinsu, yawan wakokinsa, kudaden da yake kashewa wajen biyan kafafen yada labaru da babban burinsa.

An yi wannan zantawar ne a katafaren falon Ustaz din da ke kewaye da manya-manyan kabat-kabat masu dauke da littattafan Musulunci a gidansa da ke unguwar Tudun Maliki kan titin Gidan Zoo, Kano.

Aliyu Yusuf Kakaki din ne kuma ya rubuta maku zantawar. Allah (T) ya sa mu dace. A sha karatu lafiya.

TAMBAYA: Akramakallah da yake yanzu ana yada karatuttukan Malam da wa'azozinsa kai tsaye ga duk duniya ta hanyar sakar sama (internet), duniya za ta so ta san tarihin sa tun daga shekarar da aka haife shi, da garin da aka haife shi da irin karatun da Malam ya yi na addini da na zamani da ayyukan da ya taba yi.

Ustaz Yusuf Ali yana ba da karatu

USTAZ DAKTA YUSUF ALI: A'uzu billahi minasshaidanir rajim. Bismillahir rahamanir rahim. Wassalatu wassalamu ala ashraful mursalin, Sayyidina Muhammadin wa'alihi wa sahabihi ajma'in.

An haife ni a garin Gaya da ke gabashin Kano a unguwar Juma Makera Gora a shekara ta 1949. Sunan Mahaifina Malam Ali. Mahaifiyata kuma Balkisu. Kuma da shekara shida na fara karatu a wajen iyayena. Daga nan na ci gaba da karatun Alkur'ani, na kuma rubuta shi sau shida da ka lokacin ina da shekaru 11. Daga nan ne na kuma shiga makarantu na Malaman ilimin addinin Musulunci, a inda na karanta dukkan wani fanni wanda ake karantawa a Afrika ta yamma- abin da ya shafi fikihu da Lugga da nahawu da hadisi da tauhidi. Sai da duk na karanta kowane littafi wanda ake karantawa a wannan bangare namu, wanda Malaman zaure ke koyarwa. Duk wannan karatu da na yi lokacin ban ma balaga sosai ba.

Daga baya ne a shekarar 1971 na shiga makarantar Sakandire ta SAS, bangaren Higher Muslim'. Na gama a shekara ta 1974. Amma kafin nan a shekarar 1973 an taba dauka ta aikin kidaya a garin Rano. Sannan a shekara ta 1976 na shiga Jami'ar bayero, ko kuma na ce Jami'ar Ahmadu Bello don a sannan ita ta Bayero tana karkashin ABU Zariya ne, a inda na karanci harshen Hausa da Larabci da Turanci da Musulunci da kuma tarihi a matakin difloma. Cikin shekara uku na gama, a shekarar 1978. A wannan dai shekara sai na sake zarcewa da karatun digiri a inda aka ba ni na karanta 'Law' (dokoki). Ni sai na ce a'a ina son dai kawai tsantsar addinin Musulunci, a inda na yi shekaru uku na samu takardar shaidar digiri na farko a fannin harshen Larabci da addinin Musulunci da kuma harshen Hausa a 1981. To a wannan shekaran ne na tafi na yi bautar kasa, kamar yadda aka saba a nan kasar. Na samu na yi a Kano a garin Wudil, na gama a shekara ta 1982. Daga baya na koma Jami'a a shekara ta 1989 na yi digiri na biyu a Jami'ar Bayero, inda na kammala 1993. Wannan digiri na biyu da na yi ya yi kyau kwarai da gaske. Masu duba jarabawa da na shiyya (external, internal exerminer and superviser) suka hadu suka daga darajar wannan digiri na biyu ya koma na Dakta (Phd) da wadansu gyare-gyare da aka ba ni.

Daga nan kuma sai maganar aiki da na yi. Na fara aiki ne a Ma'aikatar shari'a ta jihar Kano, kuma har yanzu ma ina cikinta. A 1974 a watan Nuwamba a lokacin ina da albashi N34, na soma. Na fara ne da Marubucin kotu (Court Scribe), sannan na zama Akawun kotu (Court Clerk), har dai na zama babban Akawu (Chief Clerk). Daga baya na zama Mataimakin Rajistara, na kuma zama Rijistara. Sannan a 1982 na zama 'Higher Registrar', daga nan har zuwa 1983. A 1986 aka mayar da ni Alkali mai daraja ta daya na zama 'Higher Area Court Judge'. Daga baya na zama Senior Area Court Judge, sai Principal Area Court Judge. Daga nan a shekara ta 1993 na zama cikakken Principal Area Court 1. Kuma a shekara ta 1995 na zama Upper Area Court Judge. To wannan mukami shi ne nake kai har shekarar 2004 ta zo. To a nan ne aka kirkiro wata sabuwar Ma'aikata saboda samuwar shari'ar Musulunci a jihar Kano aka ba ni shugabancinta. Aikinta shi ne bincike game da sha'anin shari'a a kotuna, a gano irin abubuwan da Alkalai ba su ganewa ko yake shige musu duhu ko yake musu wahala. To ya kasance mun ba da tabbacin shari'a ta gaskiya. Kowane bangare na kotu kuwa, ko da Shari'a Court of Appeal ne muna iya bincike mu nuna musu irin abin da za su rika yi. Kuma sannan hatta yawan shari'u da abin da ya shafi kudi da abin da ya shafi yawan ma'aikata, to duk a ofishina idan ana baukata za a zo a same su. To wannan shi ne matsayin da nake a kai a yanzu.

TAMBAYA: Akramakallah da yake ka yi fice wajen yada karatuttuka da wa'azozi da nasihohi ta kafafaen yada labarai a wannan nahiya tamu domin isar da sakon Allah ga 'yan Adam, duniya za ta so ta san kafafen yada labaru nawa kake gabatar da shirye-shirye. Kuma a halin yanzu Shehi yana kashe nawa ne wajen biyan kafafen yada labarai?

USTAZ DAKTA YUSUF ALI: to farko dai kafofin yada labarai wadanda nake gabatarwa akwai rediyon Kano, wanda tun shekarar 1972 na fara gabatar da shirye-shirye na Musulunci a wannan kafar yada labarai, tun tana NBC, wanda a wannan lokacin wakoki ne kawai nake karantawa na addinin Musulunci, wanda mai yiwuwa wata ran za so a ga irin wadannan wakokin a rubuce insha Allah. Tunda yanzu wakokina daban-daban na Larabci da na Hausa za su kai kamar iri dubu. Don tun 1964 na fara rubutawa, kuma har yau din nan ina rubutawa. Na fara da Rediyo Kano a wannan lokaci. Daga nan sai Rediyo Jigawa, sai Rediyon Tarayya FRCN Kaduna, sannan sai DITV. Sai NTA Kano, sai NTA Kaduna, NTA Jigawa, sai kuma KSTV, sai Rediyon Zamfara, sai TV na Kogi, sai kuma TV na Sakkwato. In kuma muka zo kan mujallu, a kan gaba dai ba kamar ALMIZAN, sai kuma TRIUMPH ta gwamnatin jihar Kano da ALBISHIR da ALFIJIR, wannan ita ta Ajami ce. Sannan ALMU'AMALAT da kuma DILLALIYA. Wadannan sune zan iya tunawa. Amma dai akwai gudummawa da nakan bayar a Rediyon Jamus da BBC da VOA na Amerika, duk sukan yi hira da ni a kan wasu abubuwa na yau da kullum, da ma VON. Yanzu haka ma sun zo sun dauki shirina, mun yi hira da su, jiya za su je su saka. To wadannan sune kafafen yada labaran.

Zai yi wuya na kayyade a yanzu, sai dai abin da na biya a wannan kwata da muke ciki, wacce ba ta kare ba, misali daga Yuli-Agusta-Satumba, wata uku na ba da Naira miliyan uku da dubu dari shida da sittin, a dunkule. Idan aka duba har yanzu wahalar da ake yi wajen kokarin dauka a aike musu da shi, mune za mu yi 'editing', kuma mu za mu nemo kaset a zo a dauka da kyamarori, kuma sannan su wadanda za su zo su karbi kaset din su kai sai an rika yi musu ihsani da sauransu. Abin yana da yawan gaske. Wannan dai wani kiyasi ne wanda shi ne na bayar a jumlace. Don cewa na yi yanzu zan rika biya ne kafin ma na yi. Ba wai sai na gama na biya ba. A'a kafin na fara cewa kala, to sai na biya. To wannan shi ne ya sa yanzu na san adadin kawai.

TAMBAYA: Mai karatu zai so ya san irin shirye-shiryen da kake gabatarwa a wadannan kafafe.

USTAZ DAKTA YUSUF ALI: To idan muka koma gidan rediyo su talabijin dai a dunkule dai akwai shirye-shirye wadanda na fara da su kamar DAUSAYIN MUSULUNCI, nan ma ina ciki, da ni ake yi. Sannan daren Juma'a akwai shiri na SAHABBAI. Akwai GYADAR DOGO. Akwai MAIGIDA KAN GIDA, wanda duk wadansu matsaloli na mata ake magana kansu. Wato shiri ne na fatawa, ake karanta min takarda ina amsawa. Akwai IBADAT. Akwai WANDA ALLAH YA NUFA DA ALHERI. Akwai IHYA'US SUNNA. Akwai NURUL ISLAM (HASKEN MUSULUNCI). Akwai ADABUL ISLAM. Akwai Ihya'us sunna. Akwai shirin ILIMI KOGI NE. wannan ne kadai na sani a wannan nahiya tamu wanda zai zauna a rika bugo mar waya ana masa tambaya a kan Musulunci gaba daya kan abin da ya shafi duniya da lahira. A take nake ba da amsa. Ina irin wannan shirin a hannu da yawa a Rediyo Kaduna da kuma nan Kano ILIMI KOGI, wanda duk ranar Laraba karfe 10:30 zuwa 12:00 na dare ana bugo min waya ina amsa tambayoyi na jama'a kai tsaye a game da addinin Musulunci. Ni kadai na fara wannan, wanda har yanzu ban samu wanda ya zama min na biyu ba. To bayan ILIMI KOGI NE akwai tafsiri.

TAMBAYA: Yanzu Ustaz zai iya fada mana yawan wakokin da ya yi tun daga lokacin da ya fara wake?

USTAZ DAKTA YUSUF ALI: Kai na yi wakoki game da sha'anin addini da sha'anin abin da ya shafi zaman jama'a, yadda za a warware matsalolin jama'a. Na yi kan yadda za a yi aure a kan soyayya ba wai a yi auren dole ba, misali. Na yi wakoki daban-daban sun kai dubu. Kuma da yadda muke yi duk wani abu idan ya faru a duniya sai mun wake shi. Kuma ni Sakatare ne har yanzu na shahararriyar kungiyar mawaka ta Hikima Kulob, wanda da Alh. Mudi Sifikin shi yake shugabancinta. Da ya sauka sai Abdullahi Sani makarantan Lungu ya shugabance ta, yanzu haka shi ne Shugabanta nine Sakatare.

TAMBAYA: Akramakallah Allah ya azurtaka da yawan mata da 'ya'ya har guda nawa ne?

USTAZ DAKTA YUSUF ALI: Yanzu ina da mata uku ne. Akwai Hajiya Hindatu da Hajiya Rabi da Hajiya Khadija. Sai kuma 'ya'ya guda 27. A cikinsu mata 14, maza 13, jikoki kuma guda hudu.

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam za ka ga dan Adam a rayuwarsa ta duniya yana da wani buri da hadafi da yake so ya cimma, ko Malam yana da wani buri ko hadafi da yake so ya cimma?

USTAZ DAKTA YUSUF ALI: To ni dai tun farko da ma burina shi ne na zama mai wa'azi. In dai na zama mai wa'azi ina ga burina ya cika, don kuwa saboda ko da jarabawa zan dauka ta Sakandare a takardar tambayoyi (question paper) ko kuma 'timetable' na jarabawa abin da zan fara jarabawa, in dai na ci jarabawan nan, ni abin da nake so kawai in yi wa'azi. Allah ina so in zama na daya don in cancanci yin wa'azi don izininka, to sai ka ga na yi na daya. Wato kodayaushe, in sallah na yi, Allah ka sa in zama mai wa'azi. Aikina kenan. Kai ma na rubuta waka a cikin rubuce-rubucena a 1974, a inda na nuna cewa, na fito da abin kuru-kuru cewa ni fa wa'azi shi ne kawai na zaba ya zama shi ne sana'ata, ya zama shi ne aikina, don na lura shi ya fi moriya, kuma ban damu ko a yarda ko kar a yarda ba. Kuma ba wai ina neman lada bane. Ni dai haka kawai na ji dai ina so na yi, ni dai in kwaikwayi aiki irin na Anbiya (Annabawa), kamar yadda na fada a wani baiti. Kuma ko a wuta aka sa ni, na ce sai na yi wa'azin. To ka ga kenan wa'azi shi ne daman abin da ya kasance burina. Sai ga shi kuma Allah ya cika min, ya zama ba wanda ya kai ni a yanzu. Don duk hanyar da ake bi a yi wa'azi na bi ta. Bayan wadanan abubuwa da na fada, ai duk watan maulidi kuma akwai gayyace-gayyace wanda ake yi min, wanda za a ba ni maudu'i in zo in yi lacca. Na gabatar da laccoci a makarantu tun daga kan Jami'a irin su Ahmadu Bello zuwa su Bayero, irin su ATC, ka taho kuma Sakandire na mata da maza. Sannan kuma ga na kungiyoyi iri daban-daban, wanda duk watan maulidi,wanda in ya zo nakan samu gayyata, wani lokaci kamar 700, kuma yawancinsu duk ina halarta, kuma kowanne akwai maudu'i wanda za a ban, wanda zan zo na yi magana a kansa.

To haka nan rayuwata take. Kuma a kodayaushe bayan wadannan karatuttuka da nake yi a kafofin yada labarai, kuma kullum waya ce, ina kuma da su sun kai kamar wajen goma daban-daban. Kuma kowane waya za a bugo tambaya, fatawa ake. Kuma kamar yadda ka gani akwai littattafai, mun ware musamman wanda ake rubuto fatawa muna amsawa, to haka nan kullum.

To, amma kuma da na ci gaba sai na ga ina da wani burin har yanzu. Daman ka san shi dan Adam, idan ka ba shi (kamar yadda Annabi (SAW) ya ce), jeji guda na zinari, sai ya yi fatan kuma ya sami na biyu. In ka ba shi kum sai ya yi fatan ya samu na uku. Burina kuma shi ne yanzu nake so musulmi, kai har da wadanda ba musulmi ba su fahimci Musulunci yadda Allah ya saukar wa Manzon Allah (SAW), yadda Annabi ya yi shi, yadda sahabbai suka yi shi, yadda kuma su malamai suka fahimta, musamman mujtahidai din nan guda hudu da sauran ma wasu mazhabobin. Saboda addinin Allah mai sauki ne. Ya zama cewa an fahimce shi, to sauran sabani babu shi a duniya sam-sam. In ka ga sabani, to sai son zuciya. Amma in dai sabani a kan addini ne, to babu shi. Don kuwa saboda "ikhtilafil umma rahama," ba ka da wani abu da za ka riko na wani nafsi ka zo ka ce da wani mai salla kafiri ne ko wani mai karatu kafiri, ba ka da wannan nafsin. To amma rashin fahimtar Musulunci da aiwatar da shi yadda Annabi ya yi da sahabbansa, wannan dai duk shi ya kawo mana haka. To burina na ga cwa an fahimci wannan. Shi ne ya sa ka ga ban karkata ga wata kungiya ko darika, ko wani tunani ba.

TAMBAYA: Akramakallah ko me za ka ce game da kaddamar da shari'ar Musulunci da wasu jihohi suka yi a nan Arewa a matsayinka na ma'aikacin shari'a?

USTAZ DAKTA YUSUF ALI: To abin da zan ce shi ne duk musulmi yana son shari'ar Musulunci, saboda haka kwarai da gaske na yi murna kamar yadda sauran duk musulmi suka yi murna. Sai dai kawai abin da nake kira shi ne a kara kyautata niyya. Wadanda suke shugabanin shari'a da wadanda suke yin shari'ar nan su kyautata niyya, wato su Alkalai da ma'aikatan shari'a sun sami kansu a cikin wannan shari'a. An ce su zo su yi wannan shari'a, to amma wadanda su kuma suke shugabanni wadanda sune ragamar jan shari'ar take hannunsu, to sune nake ganin cewa akwai gyara. Akwai rashin iklasi, wato yi don Allah. Akwai kuma sakaci wajen ganin cewa shari'ar ta dore, wato ga kotuna ga Alkalai, amma akwai rashin daurin gindi sosai da sosai irin yadda su Alkalai za su yi shari'arsu, wato gaba gadi ba tare da wani abu ya dame su ba.

Alal misali 'yan sanda ba na Alkalai bane na gwamnatin Tarayya ne, ita kuma gwamnatin Tarayya ba musulma ce ba, to ka ga akwai cikas kenan. Wanda zai kawo mai laifi, shi kansa bai yarda da abin da kake yi ba, ko kuma yawancinsu ba musulmi bane, kuma albashinsu ba yana tafiya bane a kan wannan tsari na shari'a. Saboda haka muke fatan cewa ya zama an samu abin da zai karfafi shari'ar. A samu kowace jiha ya zama tana da 'yan sandanta, kuma a yi wata ka'ida irin yadda ba za a samu zalunci ba. Dama gudun zalunci shi ne ya sa aka ce duk su zama na Tarayya gaba daya. To ina ganin in aka samu 'yan sanda na jiha ka ga kowace jiha za ta dauki 'yan sandan nan a matsayin za su yi wa shari'a ne aiki. Kuma har yanzu Alkalai su yi ta iyakacin kokarinsu, ba kawai yanke hannu da kashe mutane ba, a'a duk sad da aka samu shubuha kawai kar su damu su wai sai dole sun burge, sai sun yi shari'ar da za a yanke hannu ko a jefe mutum. A'a shari'ar nan ta Allah ce. Allah ne ya ce ga yadda za a yi ta, Annabi (SAW) ya nuna mana tsari na shari'a, cewa yadda ake yin ta shi ne mutum fa zai zo gurin Annabi ya ce ya yi zina, Annabi ya kau da kansa. Ya sake juyowa ta nan ya ce ya yi fa zina a yi masa haddi, Annabi ya ki. Ya sake dawowa har sai ya yi sau hudu, sannan har yanzu Annabi bai zai yarda a yi masa haddi ba, sai ya tuhume shi, shin kai ka sha giya ne? Ya ce shi ba abin da ya sha na maye. Mahaukaci ne kai? Ya ce shi ba mahaukaci bane. Sai Annabi ya rasa hanyar da zai bi, ya ce to shi kenan je ka a name ka. In bai dawo ba shi kenan. In ya dawo kuma, to sannan Annabi yake cewa a jefe mutum. To ka ga kenan duk sad da Annabi ya ce ku ajiye haddi kar ku yi haddi matukar an samu shubuha, kamar an samu nukuda guda 99 suna cewa mutumin nan a jefe shi, ko a tsayar masa da haddi, amma daya akwai shakka, to shi kenan kawai kada a jefe shi. Ko da kuwa an ba da shaida ne game da zina, shedu hudu sun tabbata, amma daya ana shakkar shaidarsa, to kawai sai a kori karar. To kar a dauka wannan gazawa ce. Wannan ita ce Musuluncin. Haka za a nuna wa mutane Musuluncin, ba wai alla-alla yake ya kashe mutane ba.

To idan an gane haka shi kenan. Amma ba wai a yi garaje don burgewa a yanke hukuncin jifa, daga nan har wata kotu ta gano ba haka bane. Shi kenan, wannan yana karawa shari'a rauni. Wannan shi ne abin da nake so na yi kira a kai.

TAMBAYA: Akramakallah, na gode.

USTAZ DAKTA YUSUF ALI: Ni ma na gode kwarai da gaske.

Komawa babban shafinmu                   Komawa saman wannan shafin