Ihya'us Sunna ta yi bikin saukar karatu Filin Shirin asmsa tambayoyin masu sauraron daga Ustaz Yusuf Ali

Filin amsa tambayoyin masu saurare daga Ustaz Yusuf Ali
Lahadi 22 Rabi'us Sani, 1424                



 Maigida da Uwargida | TAMABAYA TA 1  | TAMBAYA TA 2 | TAMBAYA TA 3 | TAMBAYA TA 4 | TAMBAYA TA 5 | TAMBAYA TA 6 | TAMBAYA TA 7 
Ilimi Kogi Ne | TAMBAYA TA 8
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
Labarun Ustaz Yusuf Ali:

Ihya'us Sunna ta yi bikin saukar karatu

Daga Ali Kakaki

A ranar Talata 27/3/1424 ne, makarantar Madrasatul Ihya'us Sunna, da ke unguwar Tudun Maliki Kano, ta yi gagarumin bikin saukar karatun Alkur'ani mai girma karo na farko wanda aka gudanar da shi a harabar masallacin Shaikh Dakta Yusuf Ali.

Wakilinmu, wanda ya samu halartar bikin saukar karatun, ya shaida mana cewa; dalibai mata guda uku ne na makarantar suka sauke Alkur'ani, sai namiji guda daya, wanda Allah (T) ya ba shi ikon haddace Alkur'ani, mai suna Ahmad Yusuf Ali.

Sauran dalibai mata da su ma suka samu nasarar yin sauka a wannan ranar sune; Rukayya Yusuf Ali, Amina Yusuf, da kuma Ummu Kulsum Yusuf.

Da yake jawabi a madadin Sarkin Kano bayan daliban da suka yi saukar sun karanto suratul Fatiha da wasu ayoyi daga cikin bakara a gaban dimbin jama'ar da suka samu halartar bikin, Wamban Kano, Alhaji Abbas Sunusi, ya gode wa Allah (T), da ya nuna masa wannan rana.

Ustaz Yusuf Ali yana tafsiri a masallacinsa. Cikin masu sauraro har da Dk. Umar Ganduje, Mataimakin Gwamnan jihar Kano (na biyu a zaune kan kujera daga hagu)

Ya ce yana cikin farin ciki da ya samu kansa wajen wannan bikin na saukar Alkur'ani, inda ya yi fatan alheri ga daliban da suka samu nasarar yin saukar. Wadanda kuma ba su samu sa'ar saukewa ba daga cikin daliban ya yi musu addu'ar Allah ya ba su iko su ma su sauke a nan gaba.

A karshen jawabin na Wambai, ya yi addu'ar Allah (T), ya saka wa Shaikh Yusuf Ali da dukkanin nau'o'i na alheri, musamman saboda assasa wannan makarantar ta Ihiya'us Sunna da ya yi.

A nasa jawabin, Shugaban makarantar Shaikh Yusuf Ali, ya tabo tarihin kafuwar makarantar ne, inda ya ce shekaru biyar kenan da ya kafa makarantar, inda ya yi mata tsari mataki-mataki tun daga Naziri, Firamare da Sakandire har dai zuwa Jami'a, "da yaddar Allah," in ji Shehin.

A karshen jawabin na Dakta Yusuf Ali, ya yi fatan Allah (T), ya saka wa dukkanin jama'ar da suka halarci bikin da alheri, da fatan Allah ya ba su albarkar Alkur'ani mai girma.

Kadan daga cikin daruruwan jama'ar da suka je wurin, akwai Limanin Hotoro, Malam Iliyasu, Malam Hadi, Na'ibin masallacin Murtala, Malam Ishak da kuma Alhaji Ibrahim Bako.

Komawa babban shafinmu                   Komawa saman wannan shafin