Ilimi Kogi Ne Filin Shirin asmsa tambayoyin masu sauraron daga Ustaz Yusuf Ali

Filin amsa tambayoyin masu saurare daga Ustaz Yusuf Ali
Lahadi 22 Rabi'us Sani, 1424                



 Maigida da Uwargida | TAMABAYA TA 1  | TAMBAYA TA 2 | TAMBAYA TA 3 | TAMBAYA TA 4 | TAMBAYA TA 5 | TAMBAYA TA 6 | TAMBAYA TA 7 
Ilimi Kogi Ne | TAMBAYA TA 8
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
Ilimi Kogi Ne:

Shirin Ustaz Dakta Yusuf Ali

Ayoyin jawo arziki

Mai karatu wannan shafin zai rika kawo maka shirin gidan rediyon jihar Kano mai suna Ilimi Kogi Ne da Ustaz Dakta Yusuf Ali ke yi a gidan rediyon duk mako, insha Allah. Wannan wanda aka buga a jaridar DILLALIYA ta 42 ne.

Masallacin Ustaz Yusuf Ali da ke Tudun Maliki Kano

Assalamu alaikum warahmatulLahi Ta'ala wabarakatuHu.

MAI GABATARWA: Jama'ar musulmi barkan mu da dakon sauraron mu da kuma dakon sauraron wannan shiri mai albarka, mai dimbin alkhairin gasken-gaske. Hakika yanzu kam duk wata kalma da duk wani kalami da zan yi a dangane da wannan bawan Allah, Dakta Shaikh Ustaz Yusuf Ali, bisa sadaukarwar da jajircewarsa da yake wajen bunkasa da kuma yada addinin Allah kusan in ce ta kusa karewa, don kuwa wanda duk ya yi la'akari da halin da ake ciki a wannan lokaci, ga tsananin damuna, ga kuma dare, amma Malam bai yi kasa a gwiwa ba, bai kuma gajiya ba, wajen gabatar da wannan shiri, don ba da tasa gudummawar, wajen fadakar da al'umma Ma'aiki, bisa sharudda da kuma hukunce-hukuncen addinin Musulunci. Malam ko shakka babu wannan gwagwarmaya ba dai mutum ba, sai namijin gaske, mai kaunar Allah da kuma Ma'aikin Allah. Ina ganin cewa kuma jama'a ya kamata ku ba da taku gudummawar kamar yadda kuka saba, wajen yin amfani da wannan dama da Malam yake bayarwa, domin yin tambayoyi masu ma'ana da za su karu duk al'ummar musulmi baki daya. To a yau dai akwai lambobin wayarmu guda biyu. Akwai 665801-648844. Malam barka da zuwa wannan fili.

DAKTA YUSUF ALI: Yawwa, barka ka dai.

MAI GABATARWA: To kamar yadda aka sani dai kan mu fara shirin gadan-gadan, Kano a wannan lokaci, ta yi muhimman baki domin kaddamar da wani littafi mai matukar muhimmancin gaske-gasken, kan rayuwar mai martaba Sarkin Kano, Dakta Alhaji Ado Bayero. Kuma shi kansa Malam yana daga cikin dimbin jama'ar da suka halacci kaddamar da wannan littafi. Kuma hasali ma ni kaina na je wurin. Kuma Allah Ya gane min, na ga Malam shi kansa a gaban-gaba. Na ga Malam tare da shi kansa mai martaba Sarki, tare da kuma mai alfarma Sarkin musulmi.

To kasancewar haka na ce, to ina tabbatar cewa akwai wata abu a kasa, amma dai ko meye ya faru, zan iya cewa Malam ba kai kadai ba, don kuwa kai na jama'a ne baki daya, na al'ummar musulmi baki daya, don ko ya kamata mu ga cewa ka dan zakulo mana irin wannan abubuwan da suka faru a wannan waje. Don a wannan waje gani ma na musamman na yi maka, da wani tubarau na hangen nesa, AkramakalLahu.

DAKTA YUSUF ALI: (Dariya) A'uzu bilLahi minasshaidanir rajim. BismilLahir Rahmanir Rahim. Wassalatu wassalamu ala ashrafil mursalin, Sayyidina Muhammadin wa ala alihi wa sahbihi ajma'in.

To, babu shakka wannan rana ta kaddamar da littafi, ina jin da shi mai martaba da ni ba a san wanda ya fi farin ciki ba. Don kuwa abin da ya nuna min a wannan kiran, na farko dai tukuna, ba a taba gani ba, ba a kuma taba ji ba, kamar yadda su kansu mukarrabansa, irin su mai girma Wambai, irin su Madaki, irin su Sarki Waziri, wato Sakatare, cewa ana cikin jama'a, musamman ma inda duniya ta taru haka, Sarki ya ware wani talaka, suka ce kai ko ma mai sarauta ne, a ce sad da ya kasa ya tsare mulkin nan nasa, a kuma ce a wannan halin ya kira wani ya ce zo, wato fa abin kamar yadda dai ka gani sai da ya zamo kamar Manzon Allah da Mala'ika Jibrilu, a, "Fa'asnada rukubataihi ila rukubataihi" har sai da na jingina gwiwowina a gwiwowinsa. Ko? "Zo dai," na ki, "ka zo dai, ka zo dai." To, ni na dauka ko na zauna dan nesa, sai na gurguso. Ya ce a'a na zo wajensa kawai." Saboda haka sai na zo. Da na zo ne shi ne yake cewa, sai ga Sarkin musulmi a dama da shi yana cewa, "wannan shi ne Yusufu Ali wanda kake jin labari." Wato irin kalmomin nan fa. To, amma tun da yana ji, dukkansu suna ji, "wanda kake ta ji wajen taimaka wa addinin Musulunci, a nan jiha da kasa da ma duniya baki daya," wannan lafazinsa ne. Ya ce, "saboda haka ina alfahari da shi, wannan jiha tana alfahari da shi, kuma musulmi suna alfahari da shi na wannan kasa, saboda haka ga shi nan kai ma ka rike shi amana." Wato dai ko da na wani wuri (kasarsa) kamar na je gida kenan. To, saboda haka a ci gaba da yi mana addu'a, a kodayaushe, Allah ya a yi abin lafiya a gama lafiya. Saboda haka Sarki ya fara daga hannu ya ce, "ai sai a yi mana addu'a." Wannan fa yana dariya, dariya ba wai murmushi ba, dari da farin ciki. To shi ne na yi addu'a, kuma cikin farin ciki da dariya.

To kuma shi ne mai girma Wambai yake cewa, "wannan karshen kauna kenan. Ban taba ganin Sarki ya yi wa wani irin wannan ba." To haka nan shi Sakataren Sarki, Sarki Waziri ya fada. Wannan ba komai yake nunawa ba, illa irin yadda matsayin Sarkin nan yake. In ka ga da irin yadda ake rubdugun safa da marwa a gidan nan, da takardu da kasa-kasai, na bata ni, da kuma dai abubuwa dai, wadanda tun da ma dai sun na wuce. To, amma dai a takaice dai Sarkin nan, Allah Ya nufa mai basira ne, mai hangen nesa kamar yadda yake, ka ga sai ga shi, sakamakon ya zo ya bayyana. To, saboda haka wannan murna ce da farin ciki ga dukkan wadanda suke kaunar mu, da dukkanin masoyanmu, kuma wannan karfafa gwiwa ce a kan cewa abin da muke yi din nan an sani kuma gaskiya ne. Kuma shi ne ya sa ka ga cewa, har yanzu, ka duba ka ga cewa shi ma kansa mai girma Gwamna, tunda muke karatu, mataimakin Gwamna da kuma Sarki ya tura 'ya'yansa Madaki, dukkansu su rika zuwa. Ka ga wannan duka, to mene ne kuma abin nema a kan wannan? Saboda haka muna gode wa Allah (SWT), muna yi wa Sarki addu'a, kuma tafiyar nan da zai yi gobe, zuwa Abuja, daga nan kuma ya wuce London ya yi sati uku,, to muna fata Allah (T) Ya dawo da shi lafiya, don mun taru da shi a yau din nan, a Yola, wato nan makaranta, inda aka yaye dalibai guda dari da goma, ko kuma suka sauke Alkur'ani. A nan ne yake gaya min wannan zancen.

To, kuma wannan ma har yanzu zuwan nan ma gidan rediyon nan, shi ma ka ga wannan kauna ce. To, saboda haka muna yi masa addu'a, Allah Ya kara jan zamaninsa, Allah Ya kara masa lafiya, Allah Ya kai shi lafiya da shi da abokan tafiyarsa, Ya dawo lafiya, kuma duk irin bukatun da yake so Allah Ya ba shi, ya je ya same mu lafiya. Kuma muna godewa ga wannan ziyara da ya kawo, kuma muna gode wa jama'ar Kano da suka ba da goyon baya a kan rikon nan da aka yi, da kuma a ziyarar nan ta Shugaban kasa da har yanzu aka yi ta sumul, kuma aka gama lafiya. Kamar yadda aka sani hatta ma a gidan gwamnati a gabana aka yi komai. A ran Litinin din har shabiyun dare muka kai.

MAI GABATARWA: Ba shakka wannan abu ba karamin abin farin ciki bane, a san ma da kai, a san ma me kake, a san ma kana wani abu. Saboda haka Malam wannan abu, kamar yadda ka ce wani karfi ne da kwarin gwiwa aka kara jaddada maka, duk wannan abu da kake na hidima da kake yi wa addinin Allah, wato jama suna sane, suna gani, kuma suna sauraron ka AkramakalLahu. Saboda haka wannan, abin da za mu iya cewa a kara jajircewa da damara, godiya ta musamman.

DAKTA YUSUF ALI: To, alhamdu lilLahi, madalla.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Muhammad Awwal Sharif ne daga Zariya ke magana.

Ina yi wa Shehi barka da zuwa. Kuma ina yi wa Shehu bangajiya na hidimomin da aka yi, ina kuma kara wa Shehi addu'a, Allah Ya kara wa Shehi martaba da daukaka. Ya kara kiyaye mu, Ya kara kiyaye Shehi. Allah Ya kara masa karama. Akwai tambayar da nake da ita guda daya, amma tambayar tawa shi ba a bangaren ilimi bane, a kan bangaren tarihin Shehi ne. Kwanakin baya can na karanta a wata jarida ALMIZAN, cewa Shehi sun yi karatu ne da Malam Ibrahim Al-Zakzaky na nan Zariya, ko sun zauna tare ne, to shi ne ban gane ba? Shi ya sa na ce in na bugo zan tambayi Shehi a kan dangatar sa da shi Malam din? Daga karshe kuma ina kara ma Shehi addu'a dai, ya kara hakura da jama'a, wannan martaba da aka samu, dole wanda ya samu martaba irin ta Shehi sai ya samu irin wannan. Tunda Manzon Allah (S) yana cewa, "Ashaddun nasa bala'an…" Saboda haka dole Shehi ya yi ta samun irin wannan jarrabawa, irin wannan, na wajen mutane, na wasu maganganu. WalLahi ba komai bane illa daukaka ce da kuma martaba. Kuma almajirai mun sani, kuma muna alfahari da shi, a kan wannan abin da ya yi mana. Allah Ya kara daukaka shi. To, Shehi mu biyu ne, akwai wani Aminina da yake shi ma yana wahalar samun layin, Malam Hamisu yana da sako. Ga shi: Malam ni dai ina neman barar du'a'i na neman Allah Ya yi min budi. A huta lafiya.

DAKTA YUSUF ALI: To, da farko dai game da sha'anin rayuwata yake tambaya, kuma wannan wani abu wanda aka saba, mutum yakan taso a rayuwarsa, ya yi zamani da wane da wane. Su wane ne malamansa, su wanene almajiransa, abokan hurdarsa. To ya zama lokacin ina makaranta ta sakandare, tsakanin shekara ta 1971-74, to a nan tsakanin mun zauna da shi, Shaikh Ibrahim Al-Zakzaky. Kuma ba wai kawai zama haka na makaranta ba, a'a, hulda ta addinin Musuluncin nan ta hada mu. Akwai kungiya, ta dalibai, ta makaranta, MSS. Saboda haka a lokacin ni na zama wakili ne a ciki. Wato ina da matsayi na mai duba Odita. Shi kuma ina jin ko yana Shugaba. To haka nan muka zauna. Mu 'yan kungiyar nan, da ni da shi Shaikh Ibrahim Al-Zakzaky da Muhammad Bala, wannan babban Majistaren nan, wanda yake gidan Murtala, gidansa kuma yana nan yanzu a Sharada. Wanda ina jin ko shi ne ma DPP, mai ba da umurni wajen shari'ar laifi na Jihar Kano.

To kuma da kuma Mujiburrahman. Shi ma dai ana jin sunansa. To da kuma, akwai su da dama. Mune dai kamar manyan kungiya. Shi Muhammad Bala sannan shi ya gama makarantar a sad da muka zo. Da shi ma ya zama daga cikin kungiyar, to daga baya ya zama kamar shi ne 'Patron' kamar Uban kungiya. To kuma abin da ya kara wanzarwa da wannan dangantaka, sai ya kasance mun yi hoto, hoton kuma da irin kayanmu na makaranta dai, irin farare haka nan da farar hula da bakin taguyoyi. To sai ya zama hoton yana nan. Sai wata rana haka nan sai na dauko hoton, shi na gani har ma ina jin a jaridar ALMIZAN sun ma taba karba sun buga. To wannan shi ne dangantakar.

To sannan kuma shi na biyu ko? Yana neman jalabi. To jalabi kam shi ne nema, wato a kodayaushe addu'a kashi biyu ce: Ko dai nema kake yi Allah Ya ba ka, ko kana so Allah Ya ije maka wani abin ki ko na sharri. To wannan shi ake cewa ko dafa'i ko jalabi. To saboda haka idan an ce jalabi, to abubuwa ne wanda za a yi mutum ya samu wani alkhairi na duniya da lahira. To saboda haka abin da, za a ba shi ya rika karantawa, a game da irin wannan, akwai dai ayoyi na arziki, ko karantawa ko rubutawa. wadansu hadisai ne tabbatattu na Manzon Allah (S), kamar Izawaka, kamar Alamnasharaha, kamar Ya'ayyuhal Muzammilu, da Kul a'uzu bi Rabbil falaki da Yasin, to wadannan na arziki ne. Da kuma wata aya, "Allahumma Rabbana anzil alaina ma'idatan minas sama'i takuna lana iydan li awwalina wa akhirina wa ayatan minka warzukna wa anta khairur Razikin." Da kuma "ya'atiha rizzikuha ragadan min kulli makanin." iya nan. Da kuma "wa am sik bigairi hisab." Da "inna hazha la rizikuna malahu min nafad." To wadannan ayoyi ne na arziki, ko mutum ya zama irin mai rariyar hannu din nan, ga shi yana samu, ba ba ya samu ba, amma sai ya rasa inda abin yake zuwa. Shi kuma ba shashanci yake yi ba. Amma ya danganta da girman matsalar da mutum yake ciki. In babba ce, to ya kasance ana iya rubutawa, kowacce kafa 41. In kuma matsakaiciya ce ana rubutawa kafa 21. In kuma karama ce matsalar ana iya rubutawa kafa 11.

Kuma har yanzu akwai, abubuwa wanda muke bayarwa, alal misali na sunayen nan guda shida da ake karantawa, a masallacin Juma'a kafa tamanin. Kafin lokacin da Liman yake huduba, zai iya yin salatin Annabi dari, ya kuma yi KulhuwalLahu dari. Bayan idarwa da salla kuma, ya karanta wadannan sunaye kafa tamanin. Ya Mubdi'u, Ya Mu'idu, Ya Rahimu, Ya Wadudu, Ya yaf'alu li ma yuridu, Ya Ganiyu, Ya Hamidu, Ya Mubdi'u, Ya Mu'idu, Ya Rahimu, Ya Wadudu, ignini bihalalika an haramika wa bi da'atikan an ma'asiyatika wal fadluka an mansiwak," sau tamanin. Juma'a biyar ba za ta zo wa mutum ba, sai ya wadatu, insha Allah.

Za mu ci gaba insha Allah

Komawa babban shafinmu                   Komawa saman wannan shafin