Ilimi Kogi Ne Filin Shirin asmsa tambayoyin masu sauraron daga Ustaz Yusuf Ali

Filin amsa tambayoyin masu saurare daga Ustaz Yusuf Ali
Lahadi 22 Rabi'us Sani, 1424                



 Maigida da Uwargida | TAMABAYA TA 1  | TAMBAYA TA 2 | TAMBAYA TA 3 | TAMBAYA TA 4 | TAMBAYA TA 5 | TAMBAYA TA 6 | TAMBAYA TA 7 
Ilimi Kogi Ne | TAMBAYA TA 8
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
Ilimi Kogi Ne:

Mai karatu wannan shi ne filin Ilimi Kogi da Ustaz Yusuf Ali ya yi ranar 17 ga Agustan 2002.

Tambaya ta 5

TAMBAYA: Malam Awwal ne daga Goron Dutse. Malam tambayar da nake da ita, akwai wani abokina da muke tare da shi, to a kan harkar da nake zan yi tambaya a kai. Akan dan sami kudi haka, kamar jabu guda daya zuwa guda biyu a cikin kudi, nakan bashi shawara wani lokacin daga yayin da suka zo hannunmu mu yaga su, sai ya ce, a'a tunda ba shi ya yi ba, ba shi ya sako ba, shi ba zai yarda da haka ba. Wani lokacin nakan yi nasara da shi a kan haka, wani lokacin yakan ki yarda. Shi kenan sai na gamu da shi, to yau dai muka dan tattauna da shi. Shi ne yake cewa, shi a ina ne nake nuna masa cewa yayin da suka zo hannunmu, idan muka bar su suka ci gaba, nake ga daga nan za mu yi daukar wani nauyi daga cikin wadanda suka shirya wadannan abubuwa. Sai yake nuna min bai yarda ba, shi ne na ce masa to ya saurare ni, in Allah Ya yarda zan kara neman fatawa a kan irin gyaran da na masa.

DAKTA YUFUS ALI: To na farko wanda duk ya ba da jabun nan, in ya kasance yana sani ka ga cuta ya yi. Kuma algus ne. Annabi (S) yana cewa, "man gasshana fa laisa minna," duk wanda ya yi algus, a mu'ma'amalarsa, to ba ya cikin shari'ar Musulunci, ba ya cikin wato Musulunci. Babu shakka wannan abu yana da tsoratarwa don ko saboda ko riyal daya ko dala daya ko saifa, tana iya fitarwa da mutum daga Musulunci, ka ga duk mutum rayuwarsa ta zama rayuwar banza kenan, yana amsa sunan musulmi alhali a gurin Allah shi ba musulmi bane. To saboda haka idan kuma abin nan ya zo wajenka kai ka gane jabu ne, to lallai kar ka kuma bai wa wani, ka cuce shi. Idan ka yi haka, wancan shi ba ruwansa, idan ka yi haka duk abin ya faru na wannan magana da Annabi (S) ya fada a kanka kai zai kare na biyun, wancan nasa daban, kai kuma naka daban, "walataziru waziratun ukura," kowa laifinsa daban, laifin wani ba ya hawa kan wani.

A zamanin da, sad da ake yaki na Musulunci, wani bawan Allah, ya kasance, jarumi ne kwarai da gaske, ko dai daga cikin sahabbai ko daga cikin tabi'ai dai, wato masu fadada addinin Musulunci, tun a farko-farkon nan. To kamar yadda ya saba, wato yana takama da wani doki nasa, to duk sanda ya kai hari, ko waye, duk jarumtar kafiri, sai ya kai shi kasa. Wannan dokin sai ya je, don saboda daman, yaki ba zai ba, kai tukuna da kuma abin da kake hawa. Ko da kamar mota ce ai ka ga akwai mai, sai tana da karfi, akwai batur, to haka nan ma yaki a da, da ake yin sa a kan doki, dokin shi kansa ya san ya fahimci me ake, kuma shi ke taimakawa ba da tsoro ba shi ma ya je kai ka har ka je ka kasha kafiri. To sai ran nan kamar yadda aka saba ya yi kan kafiri, sai da ya je kan zai kai mar suka, sai dokin ya kasa karasawa. Sai ya sake ja da baya ya sake bin sa, ya je kamar yadda ya saba fa, sai da ya yi haka kamar sau uku ko fiye da haka. Saboda haka ya san lallai akwai wani abin wanda ba daidai ba a tare da shi ko a tare da dokin. Sai yake jin haushin dokin, to shi ne ya dawo gida, ya kwanta barci, sai ga shi Allah Ya nuna masa wannan dokin nasa yana yi masa magana. Yana cewa, to yaya daman za ka samu kanda nake so, tunda a cikin abincina harawar da ka ba ni ka sayo akwai darhami guda daya dan jabu a ciki, to wannan shi ne dalilin da ya sa, tunda ka ciyar da ni harumun, jabu, ko da yake ba ka sani ba, saboda haka Allah Ya nuna maka sakayya. Saboda haka, idan kai kai ka zabure ne, sai in ga na kasa, in ka zabure ni sai na ji na kasa, ni na san da dirhamin jabu, to amma saboda ba zan iya magana ba, to shi ne yanzu Allah Ya yi min izini in sanar da kai. Malamai sun kakkawo wannan kissa a inda suke nuna munin jabu. Kuma irin wadannan mafarke-mafarke, sukan zama gaskiya. Kuma in dabba ta yi ma magana gaskiya ne a mafarki. Saboda haka wannan kissa da kuma hadisan Manzon Allah (S), wadanda suke nuna cewa wanda ya yi algus ba ya cikinmu, to sun isa shi wannan bawan Allah ya tabbatar da cewa, don saboda dukkanin abin da ya kuma samu da wannan sanadiyar wannan, shi dai wannan takardar jabu guda daya din nan, ta iya ba da dukkanin abin da ya samu gaba daya, abin da ya mallaka, don ko saboda lallai akwai haramun cikinsa. Kuma sannan har yanzu, idan ya yi ibada, Allah ba zai karba ba. Idan ya yi addu'a Allah ba zai karba ba, don mene? Saboda, "innama yatakabbalalLahu minal muttakina." Allah ba Ya karbar addu'ar kowa ko aikin kowa sai daga masu tsoron Allah. Idan ya yi salla za a dauka a rubuta ya yi, amma ba a karba ba. To za a rubuta masa ya yi addu'a, amma ba a karba ba. Don me saboda Annabi (S) ya fada, yara ma suna karanta wannan hadisi na goma, a cikin 'arba'un Annawawiya', cewa Annabi (S) ya ce, "Allah ya ce ya umurci mutane, muminai da abin da ya umurci da abin da ya umurci Manzanni …….." har dai izuwa karshen hadisin yana cewa "summa zakara" ko? "rajulan ash'asa agbara ya dilussafara yamuddu yadaihi, Ya Rabbi-Ya Rabbi, wa mad'amuhu haramun, wa masharabuhu haramun, wa malbasuhu haramun, wa guziya bil haramun, fa anna yustajamu lahu?" Har Manzon Allah ya ambaci wani mutum birgiza ya yi doguwar tafiya, ya mika hannunsa yana cewa, "Ya Rabbi-Ya Rabbi, amma abincinsa, haramun ne. Abin shansa haramun ne, tufansa haramun ne, an ma ciyar da shi haram," a bai sani ba ma, to Manzon Allah ya ce, "to yaya za a amsa masa?" Kenan idan ya kasance akwai haramun a cikinka ko a tufanka, to ka tabbatar da cewa Allah (T) ba zai karbi addu'arka ko kuma ba zai karbi aikinka ba.

Komawa babban shafinmu                   Komawa saman wannan shafin