'Nada Ustaz Yusuf Ali Darakta ya dace' Filin Shirin asmsa tambayoyin masu sauraron daga Ustaz Yusuf Ali

Filin amsa tambayoyin masu saurare daga Ustaz Yusuf Ali
Lahadi 22 Rabi'us Sani, 1424                



 Maigida da Uwargida | TAMABAYA TA 1  | TAMBAYA TA 2 | TAMBAYA TA 3 | TAMBAYA TA 4 | TAMBAYA TA 5 | TAMBAYA TA 6 | TAMBAYA TA 7 
Ilimi Kogi Ne | TAMBAYA TA 8
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
Labarun Ustaz Yusuf Ali:

Nada Ustaz Yusuf Ali Darakta ya dace

In ji Sarkin Kano

Daga Ali Kakaki

Sarkin Kano, Alhaji Dakta Ado Bayero ya bayyana nadin da aka yi wa Ustaz Dakta Yusuf Ali a matsayin Darakta mai binciken yadda Alkalan kotunan shari'ar Musulunci na Jihar Kano suke gudanar da shari'o'insu a matsayin abin da ya cancanta kuma ya dace kwarai da gaske.

Da yake jawabi a madadin Mai martaba Sarkin, Ciroman Gwale, kuma babban dan Sarkin na Kano, ya ce ya je ofishin Daraktan ne Ustaz Yusuf Ali da ke harabar Ma'aikatar shari'a ta jiha a Audu Bako Sakateriya Kofar Nasarawa domin cika umurnin Mai martaba Sarki da ya umurce shi da ya zo ya isar da wannan sako na nuna dacewa da nadin Ustaz din a wannan matsayin na Darakta.

Mai martaba Sarkin ya yi fatan Allah Ya taya Daraktan rikon mukamin da Allah (ST) Ya ba shi da gaskiya da adalci.

Ustaz Yusuf Ali yana tafsiri a masallacinsa. Cikin masu sauraro har da Dk. Umar Ganduje, Mataimakin Gwamnan jihar Kano (na biyu a zaune kan kujera daga hagu)

Da yake bayyana wa Ciroman Kano Alhaji Sunusi Ado Bayaro irin aikin ofishin nasa, Ustaz Yusu Ali ya ce aikin shi ne binciken dukkanin shari'o'in da kotunan Jihar Kano suka yi a kowane wata na laifi da na hakki wadanda suka yi daidai ya tabbatar da cewa sun yi daidai, wadanda akwai kuskure cikinsu ya ce ba su yi daidai ba, kuma dukkaninsu a buga a aike wa Alkalai don saboda su duba; wanda ya yi daidai su yi koyi da shi, wanda bai yi daidai ba kuma su kauce wa yanke hukunci irinsa.

Dakta Yusuf Ali ya ci gaba da cewa kowane Alkali a lokacin da yake gudanar da shari'a ta laifi ko ta hakki, sai aka samu korafi kan yadda yake tafiyar da shari'ar, to za a dakatar da sauraron wannan shari'ar, a kawo littafin shari'ar ofishin Darakta ya duba, sannan ya tabbatar cewa daidai Alkalin yake bin sahun shari'ar ko ba daidai.

Kuma sannan ya ba da shawarar yadda za a yi da wannan Alkalin ko da wannan shari'ar. "To wadannan sune kadan daga cikin ayyukan ofishin,"in ji Dakta Yusuf Ali.

Komawa babban shafinmu                   Komawa saman wannan shafin