Tambaya ta 1 Filin Shirin asmsa tambayoyin masu sauraron daga Ustaz Yusuf Ali

Filin amsa tambayoyin masu saurare daga Ustaz Yusuf Ali
Lahadi 22 Rabi'us Sani, 1424                



 Maigida da Uwargida | TAMABAYA TA 1  | TAMBAYA TA 2 | TAMBAYA TA 3 | TAMBAYA TA 4 | TAMBAYA TA 5 | TAMBAYA TA 6 | TAMBAYA TA 7 
Ilimi Kogi Ne | TAMBAYA TA 8
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
Ilimi Kogi Ne:

Mai karatu wannan shi ne filin Ilimi Kogi da Ustaz Yusuf Ali ya yi ranar 17 ga Agustan 2002.

Tambaya ta 1

Assalamu alaikum. Muhammad Awwal Sharif ne daga Zariya ke magana.

Ina yi wa Shehi barka da zuwa. Kuma ina yi wa Shehu bangajiya na hidimomin da aka yi, ina kuma kara wa Shehi addu'a, Allah Ya kara wa Shehi martaba da daukaka. Ya kara kiyaye mu, Ya kara kiyaye Shehi. Allah Ya kara masa karama. Akwai tambayar da nake da ita guda daya, amma tambayar tawa shi ba a bangaren ilimi bane, a kan bangaren tarihin Shehi ne. Kwanakin baya can na karanta a wata jarida ALMIZAN, cewa Shehi sun yi karatu ne da Malam Ibrahim Al-Zakzaky na nan Zariya, ko sun zauna tare ne, to shi ne ban gane ba? Shi ya sa na ce in na bugo zan tambayi Shehi a kan dangatar sa da shi Malam din? Daga karshe kuma ina kara ma Shehi addu'a dai, ya kara hakura da jama'a, wannan martaba da aka samu, dole wanda ya samu martaba irin ta Shehi sai ya samu irin wannan. Tunda Manzon Allah (S) yana cewa, "Ashaddun nasa bala'an…" Saboda haka dole Shehi ya yi ta samun irin wannan jarrabawa, irin wannan, na wajen mutane, na wasu maganganu. WalLahi ba komai bane illa daukaka ce da kuma martaba. Kuma almajirai mun sani, kuma muna alfahari da shi, a kan wannan abin da ya yi mana. Allah Ya kara daukaka shi. To, Shehi mu biyu ne, akwai wani Aminina da yake shi ma yana wahalar samun layin, Malam Hamisu yana da sako. Ga shi: Malam ni dai ina neman barar du'a'i na neman Allah Ya yi min budi. A huta lafiya.

DAKTA YUSUF ALI: To, da farko dai game da sha'anin rayuwata yake tambaya, kuma wannan wani abu wanda aka saba, mutum yakan taso a rayuwarsa, ya yi zamani da wane da wane. Su wane ne malamansa, su wanene almajiransa, abokan hurdarsa. To ya zama lokacin ina makaranta ta sakandare, tsakanin shekara ta 1971-74, to a nan tsakanin mun zauna da shi, Shaikh Ibrahim Al-Zakzaky. Kuma ba wai kawai zama haka na makaranta ba, a'a, hulda ta addinin Musuluncin nan ta hada mu. Akwai kungiya, ta dalibai, ta makaranta, MSS. Saboda haka a lokacin ni na zama wakili ne a ciki. Wato ina da matsayi na mai duba Odita. Shi kuma ina jin ko yana Shugaba. To haka nan muka zauna. Mu 'yan kungiyar nan, da ni da shi Shaikh Ibrahim Al-Zakzaky da Muhammad Bala, wannan babban Majistaren nan, wanda yake gidan Murtala, gidansa kuma yana nan yanzu a Sharada. Wanda ina jin ko shi ne ma DPP, mai ba da umurni wajen shari'ar laifi na Jihar Kano.

To kuma da kuma Mujiburrahman. Shi ma dai ana jin sunansa. To da kuma, akwai su da dama. Mune dai kamar manyan kungiya. Shi Muhammad Bala sannan shi ya gama makarantar a sad da muka zo. Da shi ma ya zama daga cikin kungiyar, to daga baya ya zama kamar shi ne 'Patron' kamar Uban kungiya. To kuma abin da ya kara wanzarwa da wannan dangantaka, sai ya kasance mun yi hoto, hoton kuma da irin kayanmu na makaranta dai, irin farare haka nan da farar hula da bakin taguyoyi. To sai ya zama hoton yana nan. Sai wata rana haka nan sai na dauko hoton, shi na gani har ma ina jin a jaridar ALMIZAN sun ma taba karba sun buga. To wannan shi ne dangantakar.

To sannan kuma shi na biyu ko? Yana neman jalabi. To jalabi kam shi ne nema, wato a kodayaushe addu'a kashi biyu ce: Ko dai nema kake yi Allah Ya ba ka, ko kana so Allah Ya ije maka wani abin ki ko na sharri. To wannan shi ake cewa ko dafa'i ko jalabi. To saboda haka idan an ce jalabi, to abubuwa ne wanda za a yi mutum ya samu wani alkhairi na duniya da lahira. To saboda haka abin da, za a ba shi ya rika karantawa, a game da irin wannan, akwai dai ayoyi na arziki, ko karantawa ko rubutawa. wadansu hadisai ne tabbatattu na Manzon Allah (S), kamar Izawaka, kamar Alamnasharaha, kamar Ya'ayyuhal Muzammilu, da Kul a'uzu bi Rabbil falaki da Yasin, to wadannan na arziki ne. Da kuma wata aya, "Allahumma Rabbana anzil alaina ma'idatan minas sama'i takuna lana iydan li awwalina wa akhirina wa ayatan minka warzukna wa anta khairur Razikin." Da kuma "ya'atiha rizzikuha ragadan min kulli makanin." iya nan. Da kuma "wa am sik bigairi hisab." Da "inna hazha la rizikuna malahu min nafad." To wadannan ayoyi ne na arziki, ko mutum ya zama irin mai rariyar hannu din nan, ga shi yana samu, ba ba ya samu ba, amma sai ya rasa inda abin yake zuwa. Shi kuma ba shashanci yake yi ba. Amma ya danganta da girman matsalar da mutum yake ciki. In babba ce, to ya kasance ana iya rubutawa, kowacce kafa 41. In kuma matsakaiciya ce ana rubutawa kafa 21. In kuma karama ce matsalar ana iya rubutawa kafa 11.

Kuma har yanzu akwai, abubuwa wanda muke bayarwa, alal misali na sunayen nan guda shida da ake karantawa, a masallacin Juma'a kafa tamanin. Kafin lokacin da Liman yake huduba, zai iya yin salatin Annabi dari, ya kuma yi KulhuwalLahu dari. Bayan idarwa da salla kuma, ya karanta wadannan sunaye kafa tamanin. Ya Mubdi'u, Ya Mu'idu, Ya Rahimu, Ya Wadudu, Ya yaf'alu li ma yuridu, Ya Ganiyu, Ya Hamidu, Ya Mubdi'u, Ya Mu'idu, Ya Rahimu, Ya Wadudu, ignini bihalalika an haramika wa bi da'atikan an ma'asiyatika wal fadluka an mansiwak," sau tamanin. Juma'a biyar ba za ta zo wa mutum ba, sai ya wadatu, insha Allah.

Komawa babban shafinmu                   Komawa saman wannan shafin